Huduba Ta 16

Daga Zancensa (A.S) Yayin Da Aka Yi Masa Bai’a A Madina

[A cikinta yana ba wa mutane labarin `abin da halinsu zai kasance nan gaba kuma a cikina ya kasa su gida-gida]

Raina ta yadda da abin da nake fada, kuma na dauki nauyin hakan, hakika duk wanda darussan azabobi suka bayyana gareshi karara a gabansa, to tsoron Allah kuwa ya hana shi kutsawa cikin shubuhohi.

Ku sani jarabawarku ta dawo kamar yadda take, ranar da Allah ya aiko annabisa (S.A.W), na rantse da wanda ya aiko shi da gaskiya, sai an yamutsa ku yamutsawa (jarrabba ku jarrabawa), kuma an tankade ku tankadewa, kuma sai an cakuda ku irin cakudawar nan ta kayan cikin tukunya (na dafuwa) har sai kasanku ta dawo samanku, samanku ta dawo kasanku, kuma wallahi! sai masu rigo da suka riga suka takaita sun yi rigo, kuma wallahi! sai masu rigyangyantu da suka riga suka yi rigo sun takaita.

Wallahi ban taba boye wata kalma ba, kuma ban taba yin karya ba, kuma hakika an ba ni labarin wannan matsayi da wannan rana. Ku sani! Zunubai dawakai ne masu wuyar hawa, da aka dora mahayansu, aka kuma cire musu linzami, sai ta kusa da su cikin wuta.

Ku sani! Tsoron Allah matakai ne masu kankan da kai da aka dora mahanayansu a kansu, kuma aka ba su ragamarsu, sai suka shiga da su aljanna.

(Akwai) Karya da barna, kuma kowannen yana da mutane, idan barna ta yi jagoranci to daman can ta saba yin hakan, kuma idan gaskiya ta karanta to daman hakan yakan faru, da kyar ne wani abu ya bayar da baya ya wuce sannan kuma sai ya dawo!

Daga cikin wannan hudubar [yana kasa mutane gida uku a cikinta]

An shagaltar da shi daga barin aljanna, kuma wuta tana gabansa! Da mai gaggawa mai sauri day a tsira, da kuma mai nema mai jinkiri da ya yi kauna, da kuma mai takaitawa da ya gangara wuta.

Dama da hagu masu batarwa ne, hanyar tsakiya ita ce hanya mai kyau, akanta ne sauran littattafai da kuma alamomin annabta suke, kuma daga gareta ne mashigar sunna take, kuma zuwa gareta ne kyakkyawan karshe yake.

Wanda ya yi da’awa ya halaka, kuma wanda ya yi kiren karya ya tabe, wanda ya bayyanar da sirrinsa ga gaskiya ya halaka, kuma ya ishi mutum jahilci ya zamanto bai san iyakarsa ba, babu wani mai tabbata kan asali da ya halaka akan takawa, kuma babu wata shukar wasu mutane da zata yi kishi.

Ku sitirta da gidajenku, ku gyara tsakaninku, kuma tuba tana nan, kada wani mai yabo ya yi yabo sai ga ubangijinsa, kuma kada wani mai zargi ya yi zargi sai kansa.