Huduba Ta Sha bakwai

Daga cikin maganarsa (A.S) game da wanda yake jagorantar mutane ba bisa cancanta ba

Hakika mafi zama abin ki wajen Allah mutane biyu ne: mutumin da Allah ya jingina masa al’amuransa yana mai shisshigi ga barin madaidaiciyar hanya, mai kutsawa cikin maganar bidi’a da kiran bata, kuma shi fitina ce ga wanda ya fitinu da shi,mai bacewa daga shiriyar wanda yake gabaninsa, mai batar da wanda ya yi koyi da shi a rayuwarsa da bayan mutuwarsa, mai daukar kurakuran waninsa, mai jinginuwa da kuskurensa.

Da kuma wani mutum da ya lulluba da jahilci, mai gaggawa cikin jahilan al’umma, mai bilunbituwa cikin duhun fitina, makahon (maras ganin) abin da yake cikin kulla sulhu, mutane suna kiransa masani kuma shi ba haka yake ba, ya yi asubanci sai ya yawaita tara jama’a, abin da ya karanta gunsa ya fi abin da ya yawaita, har sai ya sha ruwa wanda yake gurbatacce, ya yawaita ba tare da wani amfani ba, ya zauna tsakanin mutane yana mai alkalanci yana mai lamutar bayyana abin da ya rikitar wa waninsa, idan kuwa wata matsala ta same shi sai ya yi mata shirin shirme.

Lalatacce a ra’ayinsa, sannan sai ya yanke zartar da shi, kuma shi yana kamar sakar gizo-gizo ne a cikin abinda ya rikitar masa: bai sani ba shin ya dace ko ya yi kuskure, idan ya dace yana jin tsoron ko bai yi kuskure ba, idan kuma ya yi kuskure yana kaunar ko ya yi daidai.

Jahili mai dimuwar jahilci, ya rayu akan shirme, bai ciji ilimi ba da turmi yankakke, yana mai shikar ruwayoyi shikar nan ta iska mai busarwa, shi ba mai iyawa ba ne kan warware abin da ya zo masa, kuma shi ba mai cancanta ba ne kan abin da aka dora masa nauyinsa, ba ya sanya ilimi cikin wani abu da ya yi musunsa, kuma ba ya ganin cewa; akwai wani mai ra’ayin da ba nasa ba, Idan wani abu ya shigar masa duhu sai ya boye shi, domin ya san jahilcin kansa, ana jubar da jini saboda hukuncinsa na zalunci, kuma ana cinye gado saboda hakan.

Ina kai kukan wasu mutane da suke rayuwa jahilai zuwa ga Allah, kuma suke mutuwa batattu, babu wani abu da yafi shiga duhu a wajensu fiye da littafin Allah yayin da aka karanta shi hakikanin karantawa, ko wata haja da tafi samun shiga ko tsada fiye da littafin yayin da aka jirkita shi daga ma’anarsa, kuma babu wani abun ki a wajensu fiye da kyakkyawa, ko kuma babu wani mummuna a wajensu fiye da kyakkyawa!