Huduba Ta Sha tara

Daga maganarsa (A.S) bayan Ash’as dan Kais ya yi masa magana yana kan mimbari yana huduba

Sai ya cigaba da maganarsa akan wani abu da shi Ash’as ya  bijiro masa yayin da ya ce: ya sarkin muminai Ali (A.S), wannan akanka yake (wato; laifinka ne) ba naka ba ne (wato; ba kai ke da gaskiya kansa ba), sai Imam Ali (A.S) ya sunkuyar da kansa (ganinsa) kasa, sannan sai ya ce masa:

Me ya sanar da kai (ina ruwanka) abin da yake kaina da kuma abin da yake nawa? La’anar Allah tana kanka da la’anar duk masu la’anta! Mai saka dan mai saka! Munafuki dan kafuri! Wallahi kafirci ya taba ribace ka haka nan ma musulunci ya ribace ka! Kuma ba dukiyarka ba ko matsayinka ne ya kubutar da kai daga dayansu ba! Ka sani mutumin da ya nuna mutanensa aka kasha, ya shayar da su mutuwa, lallai ya dace na kusa ya ki shi, kuma na nesa ya ki amince masa.