HUDUBA TA 2

Imam ya gabatar da wannan huduba ne bayan ya dawo daga yakin siffain a shekara ta 38 B.H.

[A cikinta akwai ambaton halin da mutane suke akai kafin aiko Annabi (S.A.W) da siffofin Alayen Annabi (A.S), da siffofin wasu mutanen]

1-Yabo Ga Allah Madaukaki:

Ina godiyar Allah madaukaki domin cikar ni’imominsa da kuma mika wuya ga daukakarsa, da neman tsari daga saba umurininsa, Ina neman taimakonsa ina mai bukata ga isarwarsa, domin wanda ya shiryar ba ya bata, wanda ya yi gaba da shi ba ya tsira, wanda ya isar masa ba ya talauta, domin shi ne mafi rinjayen duk wani abu da aka auna, kuma shi ne mafi kyawon abinda aka taskace.

Kuma ina shaidawa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah shi kadai, shaidawa ta mai tsantsan ikhlasi, ina mai kudurce hakikaninta, muna masu riko da ita matukar mun wanzu har abada, muna masu tanadinta saboda tsoron abin da zai same mu, domin ita ce madaurin imani, mabudin ihsani, abin yardar ubangiji, kuma makorar shedan.

2-Siffofin Manzo (S.A.W);

Na shaida cewa Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne da ya aiko shi da addini shahararre, alami rubutacce, kuma littafi zananne, haske mai hudowa, fitila mai haskakawa, al’amari zartacce, mai korewa ga shubuhohi, mai kafa hujjoji da dalilai, mai gargadi da ayoyi, mai tsoratarwa da ukubobi.

3:Zamanin Jahiliyya;

Allah ya aiko shi alokacin da mutane suna cikin fitinar da aka yanke igiyar addini a cikinta, katangun yakini suka raunata, asasin addini ya tsakude, al’amura suka d’aid’aice, mafita ta yi wahala, mashiga ta makance, shiriya ta bice, makanta ta game.

Aka saba wa Allah, aka taimaki shaidan, aka ki taimakon imani, sai ginshikansa suka ruguje, koyarwarsa ta jirkice, tafarkinsa ya tsufa, hanyoyinsa suka toshe.

Sun bi shedan sai suka kutsa tafarkinsa, suka gangara

 magangararsa, da su ne alamominsa suka tafiyu, tutarsa ta tsayu (d’agu), a cikin fitinar da ta bi ta kansu da daginta, ta taka su da kofatanta, ta tsayu akan gefen kofatanta, suna masu d’imuwa da gigicewa, jahilai ababan fitina a cikinta, a cikin mafi alherin gidan da mafi sharrin makwabta, baccinsu raya dare ne, kwallinsu hawaye ne, a duniyar da malaminta an sa masa takunkumin Magana, jahilinta abin girmamawa.

4-Siffofin Ahlul- Bayt (A.S);

Su ne ma’ajin sirrinsa, madogarar al’amarinsa, kuma salkar iliminsa, makomar hukuncinsa, kogunan (taskokin) littattafansa, duwatsun (makaarar) addininsa, da su ne aka tsaida karkatar kashin bayansa (aka k’arfafe shi), aka kuma tafiyar da makyarkyatar kafadunsa[1].

[Game Da Wasu Mutane Daga Munafukai]

Sun shuka fajirci, sun shayar da shi dimuwa, sun girbi halaka.

6-Matsayin Ahlul Bayt;

Ba a iya kamanta wani daga cikin wannan al’umma da Alayen Annabi (A.S), ba kuma zasu daidaita da wanda ni’imominsu suka gudana a gareshi ba har abada. Su ne asasin addini, kuma madogarar yakini, Zuwa garesu ne mai wuce gona da iri zai koma, wanda yake na baya da su ne zai risku. Suna da hususiyyar (sun kebanta da) hakkin wilaya da mika musu wuya, wasiyya da gado nasu ne, a yanzu ne gaskiya ta dawo hannun ahlinta[2], an ciratar da ita zuwa maciratarta.


[1] - Abinda yake tsoro na karkatar da addini da batar da mutane, Wato kare addini da kuma abinda yake ji masa na tsoron karkacewa, da Ahlinsa ne (A.S) aka tafiyar da tsoron wannan aka kuma magance hakan.

[2] - Wato ya riki halifancin da Allah da Manzonsa suka yi masa wasiyya da shi.