Huduba Ta Ishirin

A cikinta yana tsoratarwa daga gafala kuma yana fadakarwa da komawa zuwa ga Allah

Ku sani da kun ga abin da wanda ya mutu a cikinku ya gani, da kun yi raki kun dimauce kun gigice, da kun ji kun yi biyayya, sai dai an kange muku abin da suka gani, kuma nan kusa za a jefa muku shamaki da hijabi! Kuma an nuna muku idan kuna da idanuwan basira, kuma an jiyar da ku idan kun ji, an shiryar da ku idan kun shiriya, kuma da gaskiya nake gaya muku: lallai darussa sun fito muku kuru-kuru, kuma an gargade ku da abin da yake akwai wa’aztuwa a cikinsa, kuma babu mai isarwa daga Allah bayan manzanni sai mutane.