Huduba Ta 21

Kalma ce da ta kunshi wa’azi da hikima

Karshen hadafi yana gabanku, kuma kiyama tana bayanku tana kora ku, ku saukaka kaya kwa riska, kuma ana saurara wa na farkonku da na karshenku ne.

(Wato wanda ya diba da nauyi ba ya sauri; haka nan wanda ya yi zunubai ba zai kai ga hadafi ba na samun rahama). (Mai sharhin Nahajul Balaga yana cewa: Bayan maganar Allah (s.w.t) da manzosa (s.a.w), da an kwatanta wannan maganar da ta bayi, da ta rinjaye su gaba daya).