Huduba Ta 22

Yayin da labarin masu warware bai’a ya zo masa

 [yana muzanta aikinsu, yana dora musu jinin Usman, yana kuma yi musu barazanar yakarsu]

Muzanta masu warware bai’a

Hakika shedan ya tara rundunarsa, ya jawo rundunarsa, domin ya mayar da zalunci cikin biranensa, barna ta dawo asalinta, wallahi babu wani mummuna da suka taba gani tare da ni, sannan kuma ba su yi mini adalci tsakanina da su ba.

Zargin Usman

Hakika su suna neman wani hakki ne da suka bar shi, kuma jinni da su suka zubar da shi, idan kuwa na kasance na yi tarayya da su a ciki, to wallahi suna da nsu rabo a cikinsa, idan kuwa su ne suka yi ban da ni, to mene ne zasu bi ni da shi, kuma mafi girman hujjarsu tana kansu, suna neman shayarwar uwar da ta riga ta yaye, suna raya bidi’ar da aka kashe.

Kaicon mai da’awa! Waye ya yi da’awa! Me zan amsa! Hakika ni na yarda da hujjar Allah a kansu, da iliminsa da su.

Barazanar Yaki

Idan kuwa suka ki, sai in ba su kaifin takobi, kuma ya isa mai warkarwa daga barna, mai taimako ga gaskiya!