Huduba Ta 23

Tana kunshe da tarbiyyar talakawa kan zuhudu, da luras da masu wadata kan tausayi

Tarbiyyar Talakawa

Amma bayan haka, hakika lamari yana saukowa daga sama zuwa kasa kamar digon rowan sama zuwa ga kowace rai da abin da aka raba mata na dadi ko ragi, idan dayanku ya ga wani dan’uwansa da wani abu haka a cikin iyali ko dukiya ko ran wani, to wannan kada ya zama masa fitina, hakika mutum musulmi matukar bai yi yaudara ba da wani mummunan hali da yake bayyana wanda yake jin tsoronsa idan aka fada, kuma ake iya jan hankalin sauran mutane da shi, to zai kasance kamar mai rabauta ne mai yalwa, wanda yake sauraron farkon yalwa ga kwanonsa da zai kawo masa wani rabo, kuma ya dauke masa wani nauyi.

Haka nan mutum musulmi kubutacce daga ha’inci da yake sauraron dayan abubuwan alheri biyu daga Allah: Imma dai mai kira zuwa ga Allah, to abin da yake wurin Allah ya fiye masa, kuma imma dai arzikin Allah, sai ya kasance mai iyali da dukiya, kuma addininsa da darajarsa suna tare da shi.

Hakika dukiya da ‘ya’ya gonar duniya ce, aiki na gari kuwa gonar lahira ce, kuma Allah yana hada su ga wasu mutanen, ku ji tsoron Allah da abin da ya tsoratar da kawukanku da shi, ku ji tsoronsa tsoron da ba na kawo uzuri ba, ku yi aiki babu riya da jiyarwa; domin duk wanda ya yi aiki ga wanin Allah, to Allah zai jingina shi ga wanda ya yi aiki saboda shi.

Muna rokon Allah matsayin shahidai, da rayuwar marabauta, da abotar annabawa.

Luras da masu wadata

Ya ku mutane, kada wani mutum –koda kuwa yana da dukiya- ya wadatu daga danginsa, da kariyarsu gareshi da hannayensu da harshensu, su ne mafi girman mutanen da suke tare da shi da ba shi kariya, kuma su ne mafi hada masa karfinsa, kuma su ne mafi tausaya masa yayin da wani abu ya faru gareshi. Kuma harshen gaskiay da Allah yake sanya shi ga mutum, ya fi masa dukiya da wani yake gadonta.

Daga Ciki:

Ku sani, kada wani ya kaucewa danginsa yana ganin suna da bukata sai ya biya musu ita da abin da koda ya rike shi ba ya kara masa komai, kuma idan ya bayar da shi ba ya rage masa komai, duk wanda ya rike hannunsa (taimakonsa) ga danginsa, to ana rike hannunsa daya ne kawai garesu, shi kuwa ana rike masa hannaye masu yawa nasu ne gareshi; wanda duk ya tausasa, to kaunar danginsa zata dawwama gareshi.