Huduba ta Ishirin da Biyar

[Ya yi wannan hudubar lokacin da labari ya zo masa cewa mutanen Mu’awiya sun mamaye garuruwa, kuma wakilansu biyu da suke Yaman suka zo wurinsa – su ne Ubaidullahi dan Abbas, da Sa’id dan Numran- yayin da Busru dan Ardat ya mamaye ta, sai ya mike tsaye kan mimbari yana mai kokawa da abin da yake faruwa na kasalar sahabbansa wurin yin yaki, da sabawarsu gareshi a ra’ayi yana mai cewa]:

Ita dai Kufa ce, ina ina rike ta in sake ta (wato ina da iko da ita), amma idan dai ba zaki kasance ce sai kamar yadda kike (na rashin biyayya gareni), iskar ki tana kadawa, to Allah ya muzanta ki!

Sannna sai ya fadi wasu baitoci kamar haka:

Ina mamaki alherin babanka ya Amru ga shi ni

Ina da dan ‘yar ragowa ce a cikin wannan kwano

Sannan sai ya ce: An ba ni labarin cewa Busra ya tafi Yaman, kuma ina jin cewa wallahi wadannan mutanen zasu ci galaba a kanku saboda haduwarsu a kan barnarsu, da kuma rarrabarku a kan gaskiyarku, da sabawarku ga jagoranku a kan gaskiya, da biyayyarsu ga jagoransu kan barna, da kuma kiyayewar amana ga shugabansu da kuma ha’incinku, da gyaransu a cikin garuruwansu, da barnnarku, (lamarin ya kai ga cewa ina jin tsoron) da na ba wa dayanku amanar kwano da na ji tsoron kada ya yi ha’incin marikinsa.

Ya Ubangiji! na gaji da su, sun gaji da ni, na kosa da su, su ma sun kosa da ni, ka musanya mini mafi alheri daga garesu, ka musanya musu mafi muni daga gareni. Ubangiji ka zaizaye zukatansu kamar yadda gishiri yake zaizayewa a cikin ruwa, ni kam wallahi na so a ce ina da mahayan doki mayaka dubu daga Banu Firas dan Ganmu. A nan ne da ka yi kira, sai mahaya daga cikinsu zo maka kamar gajimaren lokacin zafi. Sannan sai ya sauka daga kan mimbari.

Gajimaren lokacin zafi da yake babu ruwa cikinsa sai ya zo da sauri ba shi da wani nauyi da nuku-nuku.