Huduba ta Ishirin da Shida

[Yana siffanta larabawa kafin aiko Annabi, sannan yana nuna halayensa kafin yi masa bai’a]

[Larabawa kafin aiko Annabi]

Allah madaukaki ya aiko Muhammad (s.a.w) mai gargadi ga talikai, amintacce kan wahayi, ku a lokacin ya ku larabawa kuna kan mafi munin addini, da mafi munin gida, kuna masu rayuwa tsakanin duwatsu masu tsandauri, da kuramen macizai, kuna shan gurbatacce, kuna cin busasshen abinci, kuna zubar da jininku, kuna yanke zumuncinku, ga gumaka kafaffu a cikinku, ga zunubai sun kan kama a tsakaninku.

Yana mai cewa:

Sai na duba na ga ba ni da wani mataimaki sai alayena, sai na yi wa mutuwa rowarsu, sai na kanne a kan kwantsa, na sha a kan shasshakewar makogaro, na yi hakuri a kan hadiye bakin ciki, a kan mafi dacin dandanon madi.

Yana mai cewa:

Bai yi mini bai’a ba har sai da ya shardanta a ba shi kudi kan yin bai’ar, tir da hannun mai yin wannan bai’a, amanar mai sayarwa kuwa ta tozarta. Don haka ku yi riko da yaki da tanadi, ku yi masa shirinsa, wutarsa ta huru sosai, hasken wutarsa ya yi sama, ku kuma dage wa hakuri, domin shi ne ya fi daciya ga nasara.