Huduba ta Ishirin da Hudu

Tana kunshe da Tattararrun Bayanai

[A cikinta akwai halatta yakar masu sabawa da kuma kira zuwa biyayyar Allah, da daukaka a cikinta domin samun rabauta]

Wallahi ba ni da wani nuku-nuku da sassautawa a kan yakar wanda ya saba wa gaskiya, ya fada cikin barna. Ku ji tsoron Allah ya ku bayi, ku gudu zuwa ga Allah (umarni ne) daga Allah, ku kutsa cikin abin da ya tsara muku, ku tsayu da abin da ya dora muku, (idan kuka yi hakan) to Ali (a.s) ya lamunce muku rabautarku a lahira idan ba a ba ku ita ba a duniya.