HUD’UBA TA UKU

[Hud’ubarsa (A.S) da aka san ta da shak’shak’iyya tana k’unshe da kokawa game da al’amarin halifanci da kuma rinjayar da hak’urarsa gabarinta sannan mubaya’ar mutane gareshi]

Haka ne wallahi! Hak’ik’a wane ya sanya ta {kamar yadda ake sanya riga} alhalin kuma ya san cewa misalin matsayina game da ita kamar matsayin kan inji ne na nika da dutsensa, kwararar ambaliyar ruwa daga gare ni yake gangarowa kuma tsuntsu ba ya iya kaiwa wajena {duk tashinsa}, amma sai na sakaya tufafi na kau da kai[1]  na kuma cije na kawar da kai, na zama ina mai kai-kawon ko ina tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu, da babba yake tsufa a cikinsa yaro kuma yake girma a ciki, mumini yake shan bakar wahala aciki har sai ya riski ubangijinsa.

[Rinjayar Da Hakuri]

Sai na ga hakuri akan wannan ya fi lizimtuwa, sai na yi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kuma shakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa, har sai da na farko ya wuce, sai ya mika ta zuwa ga wane[2] bayansa. Sannan sai (A.S) ya kamanta misalin wakar A’asha:

Ya bambanta kwarai ranata akan bayan Taguwa

Da ranar Hayyan Dan’uwan Jabiri[3]

Abin mamaki! Yayinda ya kasance yana neman ya sance ta daga wuyansa a rayuwarsa sai ga shi ya kulla (mika) ta ga wani bayan wafatinsa, ya mamakin tsananin yadda suka yi kashe mu raba na abinda yake cikin hantsarta!![4] sai ya sanya ta cikin wani yanayi na rabo mai kaushi da rauninsa ya munana, shafarta tana kaushi, tuntube (kura-kurai) suka yi yawa a cikinta da kawo hanzari, ma’abocinta kamar mahayin shu’umar dabba ne da idan ya tsuke (jan) linzami sai ta yanke[5] (shake), idan kuma ya saki sai ya halaka, {musamman saboda tutsu, ko fad’owa}.

sai aka jarrabci mutane –Na rantse da Allah- da kaucewa da tutsu (ga barin hanyar shiriya) da jirkicewa da karkacewa (daga tafarki madaidaici)

Sai na yi hakuri tsayin lokaci, da tsananin jarabawa, har sai da ya wuce shi ma sai ya sanya al’amarin halifanci a hannun wasu jama’a da ya raya cewa (wai) ni daya ne daga cikinsu. Kaicon al’amarin shura!, yaushe ne kokwanton fifikon al’amarina akan na farkonsu[6] ya faru har da zan zama ana gwama ni a tsaran makamantan wadannan! (abokan shura) Sai dai ni na kasance ina yin kasa-kasa idan suka yi kasa-kasa, in tashi sama idan suka tashi, sai ga wani daga cikinsu ya karkace saboda gabar da take zuciyarsa, wani ya karkata ga surikinsa, saboda kaza-da-kaza. {Ai saboda akwai manufofi da suke boye da ba zan so ambatonsu ba}.

Har sai da na ukun mutanen[7] ya tsayu da iko (ya samu halifanci) yana mai mike awazunsa, tsakanin turosonsa[8] da makiyayarsa[9], (wato kece raini da handama da ba-ba-kere, da watanda da dukiyar al’umma, kamar ana ci ne ta baka yana fita ta duwainiya, wannan misali ya fi karfi da nuna munin abin fi ye da a ce ana ci yana zuba ta baka) ‘ya’yan babansa (Wato ‘yan kabilarsa Banu Umayya) suka mike tsaye tare da shi, suna cin dukiyar Allah irin cin da rakumi ya ke yi wa tsiron karmamin bazara. Har kwanansa suka kare, sakamkon aikinsa ya same shi, katon cikinsa ya kifar da shi akan fuskarsa.

[Bai’a Ga Imam Ali A.S]

Ban Ankara ba sai ga mutane sun gaggauta zuwa gareni kamar gashin wuyan kura[10], suna cuncirindo akaina ta kowane janibi, har aka take hasanaini[11], aka yaga mini gefen tufafi saboda zozayya, suna masu kewaye ni kamar garken tumaki.

Yayin da na tsayu da lamari sai wata jama’a ta kwance alkawarin bai’a[12] wata kuma ta fita daga jama’a[13], wata kuma ta zama azzaluma[14], kamar ba su ji fadin nan na Allah madaukakin sarki ba cewa: “Wannan gida ne da muke sanya shi sakamako ga wadanda ba sa son takama a bayan kasa balle fasadi kuma kyakkyawan k’arshe yana ga matsu tsoron Allah.” A’a wallahi! sun ji wannan kuma sun hardace ta akansu, amma sai dai duniya ta k’awatu a idanunsu, kuma adonta ya yi musu k’aye!.

Amma na rantse da wanda ya tsaga iri! ya halitta halitta, ba domin halartar masu halartar bai’a ba, da kuma tsayuwar hujjar samun masu taimakawa ba, da kuma alkawarin da Allah ya daukar wa malamai da cewar kada su tabbatar da jur’ar nan ta handamar (ba-ba-keren) azzalumi, da bak’in cikin yunwar nan ta (handame hakkin) abin zalunta, da na jefa igiyarta akan kafadunta[15] da na shayar da na karshensu[16] abinda na shayar da na farko[17] da kun sami wannan duniyar taku a wajena ba ta kai k’imar fyaciyar akuya ba[18].

Masu ruwayar huduba suka ce; Sai wani mutum  daga mutanen Sawadi[19] (Iraqi) ya mike zuwa gareshi yayin da ya kai daidai nan a hudubarsa, ya mika masa wani littafi, sai ya ringa dubawa cikinsa, yayin da ya gama sai Dan Abbas ya ce da shi: Ya Amirilmuminin! da ka ci gaba da (koro) maganarka daga inda ka gangaro. Sai ya ce: Ba zai yiwu ba Ya Dan Abbas! Wannan k’ok’iya[20] ce da ta yi ruri da gunji sannan sai ta nutsa ta koma!.

Dan Abbas yana cewa: Ban taba bak’in ciki akan wata Magana ba da ta kub’uce mini kamar bak’in cikina akan wannan maganar da cewa ina ma dai Amirilmuminina (A.S) ya ci gaba da ita zuwa inda ya yi nufi.


[1] - Kamar yadda akan sakaya labule domin shamaki daga abu, haka nan imam Ali ya kawar da kai ya rufe idonsa ya cije ya hakura.

[2] -Usman Dan Affan

[3]-Labarin Hayyan Danuwan Jabiri shi ne: Hayyan da Jabir ‘ya’yan Assimin mutanen Hanafiyya, hayyan ya kasance mutum ne mashayi kuma abokin kwalewar Al-a’asha ne, dan’uwansa Jabir ya fi shi karancin shekaru, wata rana Hayyan ya ce da A’asha: Ka danganta ni zuwa ga dan’uwana alhali ya fi ni karancin shekaru! Sai A’asha ya ce: Cika makil da na yi ne ya sanya ni bisa tilas na aikata haka, sai Hayyan ya ce: Wallahi! Ba zan sake zama da kai wajan sha ba har abada matuk’ar ina raye.

Shi ya sa A’asha ya yi wannan baiti yana nuna halin da ya fada saboda rabuwarsa da Hayyan yana cewa: Bambanci ya girmama tsakanina da Hayyan dan’uwan Jabir yayin da nake cikin rana mai tsanani akan rak’uma shi kuma yana can kan teburin giya yana maye yana hutawa da k’walewa, cikin yalwa da shakatawa da kwanciyar hankali-------

-----Haka nan halifancin na farko da na biyu ya bambanta da na imam Ali (A.S) yayin da nasu ya kasance cikin kwanciyar hankali da rashin rarrabuwa da karfin daula, shi kuma nasa ya kasance cikin yake-yaken cikin gida da jarrabawoyi da rashin kwanciyar hankali da fitintinu da rarrabe-rarrabe.

[4]- Kashe mu raba kan rike min kahonsa in tatsa in na gama sha in ba ka.

[5] - Kamar mai hawan rakuma idan ya ja ya shaketa sosai sai hancinta ya yanke ya katse, domin ita zata yi ta fincikar kanta ne har ta katse hancin, idan kuma ya sake ta domin kada ya takura ta sai ta kutsa da shi ya kasa mallakarta ta watsar da shi har ya halaka ko ya karye ko ta taka shi da makamanta haka.

[6]-Shi ne Abubakra Dan Abi Kuhafa.

[7]- Na uku shi ne Usman Dan Affan.

[8] - Kashinsa.

[9] - Wajan cin abincinsa.

[10] - Ana buga misali da gashin wuyan kura saboda cinkoso da taruwa waje daya.

[11] - Imam Hasan da Husaini (A.S)

[12] - Aisha da Talha da Zubair.

[13] - Hawarijawa.

[14] - Mu’awiya da mutanensa.

[15] - Da na bar musu mulki na hakura daga igiyarsa na jefa ta akansu.

[16]- Kamar Mu’awiya da jama’arsa da Aisha da jama’arta.

[17] - Kamar yadda na kyale halifofin farko guda uku da suka yi mulki saboda rashin samun cikar sharudda kamar masu taimakawa, da haka ne da na bar wa Mu’awiya da ire-irensa sun ci gaba da mulki.

[18] - ‘Yar majinar da akuya takan fyato ta daga hancinta, domin ta samu walwala akanta.

[19] -  Sawad yana nufin baki, larabawa sukan kira dajin da yake kore shar da baki, tunda kasar irak’i koriya ce shar sai suke kiranta da sawad, wato bakar kasa.

[20] - K’ok’iya wani abu ne ja kamar wuta da yake fita daga rakumi ko taguwa yayin da take wani ruri, sannan sai ta nutsa ta koma bayan sun nutsa sun dakata.