HUDUBA TA HUDU

[Tana daga cikin mafi fasahar maganarsa (A.S), yana mai yi wa mutane wa’azi acikinta yana tsamar da su daga bata zuwa shiriya, ana cewa ya yi ta ne bayan kashe Dalha da Zubair]

Da mu ne kuka shiriya (kuka gane hanya) a cikin duhu, kuka kuma hau k’ololuwar d’aukaka, saboda mu ne kuka fita daga duhu, Allah ya toshe kunnuwan da ba sa jin tsawatawa! yaya zai yiwu wanda tsawa ta kurumta ya ji ‘yar murya,[1] duk zuciyar da ba ta bar tsorata (tsoron Allah) ba, to ta k’arfafa.

Ban gushe ba ina sauraron sakamakon yaudara ya same ku, kuma ban gushe ba ina ganin ku da siffar nan ta mayaudara, rigar addini ce ta kare ni daga gareku, kuma kyautata niyyata ya nuna mini hakikaninku, na tsayar muku da hanyar gaskiya a cikin tafarkin nan na bata, sai ga shi ku kuma kuka kasance kuna haduwa da ni babu dalili, kuna ta haka da ba zata cimma ruwa ba.

A yau ne zan sanya dabbobi ma’abociyar fasaha ta yi muku magana[2], tir da ra’ayin mutumin da ya saba mini, ban taba kokwanton gaskiya ba tun da aka nuna mini ita, ku sani musa bai ji tsoro saboda kansa ba, ya ji tsoron rinjayen jahilai ne da daular batattu[3]! A yau muka hadu (taho mu gama) akan tafarkin gaskiya da na bata, domin wanda ya sami nutsuwa da samun ruwa ba zai ji kishirwa ba!.


[1] - Wato duk wanda ba ya jin gargadi ya ya za a yi ya ji nasiha.

[2] - Ai na nuna wa duniya sirrinku da kuka boye.

[3] - Imam Ali (A.S) ba ya jin tsoro saboda kansa, a’a tsoronsa irin na musa (A.S) ne.