HUDUBA TA BIYAR

[Daga maganarsa yayin da aka karbi ran manzon Allah (S.A.W) Abbas da Abu Sufyanu suka yi masa Magana akan su yi masa bai’a kan halifanci, wannan kuma ya faru ne bayan an riga an gama yi wa Abubakar bai’a a Sakifa, a cikin Hudubar yana mai hani ga fitina, yana kuma bayyana dabi’arsa da iliminsa]

[Hani Ga Fitina]

Ya ku mutane! Ku keta ta cikin ambaliyar fitina da jirgin tsira, ko karkata ga barin hanyoyin k’iyayya, ko sanya hulunan alfahari. Wanda duk ya tashi sama da fukafuki ya rabauta, ko kuma ya mika wuya sai ya hutar, ruwa ne mai jirkita,[1] kuma lomace da take shake mai hadiyarta, kuma mai debe ‘ya’yan itaciya ba a lokacin nunarta ba kamar mai shuka ne ba a kasarsa (gonarsa) ba.

 [D’abi’arsa Da Iliminsa]

Idan na yi magana sai su ce: Ya yi kwad’ayin mulki, idan na yi shiru sai su ce ya ji tsoron mutuwa! A’aha wallahi! Sam ba haka ba ne! bayan faruwar ‘yar waccan[2] da waccan d’ayar[3]!, wallahi! D’an Abi d’alib ya fi nutsuwa da mutuwa fiye da nutsuwar jariri da nonon babarsa, a’aha! tabbas kad’ai ya tattare a cikin b’oyayyen ilimin da, da na bayyanar da shi da kun d’imauce kun raurawa irin raurawar igiya a cikin rijiya mai zurfi.

Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria
hfazah@yahoo.com

[1] - Halifanci da al’amuran tafiyar da sha’anin mulki da al’umma.

[2] - ‘Yar waccan: fadinsu cewa ya yi kawadayin mulki.

[3] - 34- waccan dayar: fadinsu ya ji tsoron mutuwa.