HUDUBA TA SHIDA

[Yayin da aka yi masa nuni da kada ya bi Dalha da Zubair, kuma kada ya yi fakon yakarsu, a ciki akwai bayanin siffarsa da cewa shi (A.S) ba ya yaudara]

Wallahi ba zan zama kamar kura ba, da take kwana tana mai ruri da gunji, har mai nemanta ya riske ta, mai fakonta ya cafke ta, sai dai ni ina dukan mai juyawa ga barin gaskiya (ta hanyar amfani) da mai gabatowa zuwa gareta, mai sabo mai kokwanto kowane lokaci kuwa (in ture shi) da mai biyayya, har mutuwa ta zo mini.

Wallahi ban gushe ba abin tunkudewa gabarin hakkina, ana zabar wasu da fifita su a kaina, tun lokacin da Allah ya karbi annabinsa (S.A.W) har zuwa ranarmu wannan.