Huduba Ta 7

[Yana sukan yin biyayya ga Shedan; abin nufi da Shedan wani mutum ne]

Sunriki shedan mai mallaka da jibintar lamurarransu, shi kuma ya rike su karnukan farautarsa, sai ya yi kwai y akyankyashe a zukatansu (kirazansu), sannan sai ya yi rarrafe ya yi yawo a dakunansu, sai ya kalli idanuwansu, ya yi magana da harshensu, ya dora su kan kurakurai, ya kuma kawata musu sabo, suka yi aiki na wanda shedan ne ya yi tarayya da shi a ikonsa, kuma ya yi maganar barna da bata ta harshensa!