DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI  JINKAI

TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA MANZON RAHAMA

DA ALAYENSA TSARKAKA

Ahlul Baiti (A.S) a cikin Kur’ani mai girma:

 “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya kuma tsarkake ku tsarkakewa”

Surar Ahzab\ aya: 33

Ahlul Baiti (A.S) a cikin hadisai madaukaka:

 “Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su”

Sahihan Littattafai Da Masanid

Imamanci Da Nassi

Allah ya halicci mutum bisa dabi’a da daukar mataki da iya daukar nauyi da zai iya kai shi ga halifancin Allah a bayan kasa, ba zai yiwu ga kowane mahaluki ba ya iya wannan al’amari koda kuwa mala’ika ne domin su an umarce su da su yi sujada gareshi. A wani bangaren kuma mutum yana mallakar wata nau’in dabi’a da takan iya hana daukakarsa da cigaban kamalarsa.

Wannan mutum yana dauke da siffofi madaukaka ta wata fuska da kuma siffar karkata zuwa ga kaskancin karkata a gefe guda, abin da yake nuna cewa shi abin halitta ne daya da yake mallakar nufi da ‘yanci akan ya zabi aiki mafi karfi da kuma mataki da ya dace domin gina rayuwarsa.

An bai wa mutum wannan ne domin ba shi damar motsawa a dukkan sasanni mafi fadi da yake keta duniyar mariskai zuwa sama da hakan da kuma nuna cewa samuwarsa tana da wani hadafi da hannun kudura ya zana shi. Ba a halicce shi don wasa ba, ba a kuma bar shi haka nan ba kamar yadda ambato mai hikima ya fada yayin da ya ce: “Shin kuna tsammanin mun halicce ku da wasa kuma ku ba masu komowa ne zuwa garemu ba[1]”.

Ba kawai mutum ne shi kadai yake motsi cikin wannan samuwa ba cikin wannan hadafi da kuma tsari da aka shirya shi, akwai sauran halittu da suke tarayya da shi a wani bangare da nassin Kur’ani mai girma yake cewa: “Ba mu halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu ba muna masu wasa[2]”. Idan ya tabbata cewa halitta dukkanta tana tafiya da hikima da juyawar Ubangiji daga cikinta akwai mutum, kuma dukkansu masu tafiya ne zuwa ga cimma wani hadifi da ake bukata kuma cewa kowane abu yana da shiriyarsa, to menene iyakar hadafin da saboda shi ne aka halicci mutum?

Kur’ani mai girma yana iyakance wannan da hadafin da aka halicci mutum saboda shi da fadinsa: “Ban halicci mutum da aljani ba sai don su bauta mini[3]”. A nan zamu yi la’akari da cewa kalmar taskacewa da togewa (sai don) tana nufin Allah ba shi da wani hadafi da manufa na halittar mutum sai ibada, kalmar don su bauta min tana bayanin sababi da dalilin halitta shi ne, wato mutum halitta ce don ibada ga Allah, Amma tambaya a nan ita ce: Idan hadafin halittar mutum yana takaituwa ne a ibada ba wani abu ba to mecece ibada? Menene kuma hakikaninta?

Idan hadafi na karshe na halittar mutum shi ne kusancin Allah da bauta da dan Adam yake samun kamala da ita, to menene yake tunkuda shi domin zuwa ga isa zuwa wannan kamalar?

Hakika mutum a dabi’arsa da fidirarsa suna riskar cewa bukatarsa tana zama ta hanyar da zai iya toshe tawayar da take samunsa, kamar yadda ya ke riskar bukatarsa ta hanyar abubuwan da sukan iya kai shi ga kamalarsa sai ya motsa domin nemanta, sai dai tambaya a nan ita ce: Ta yaya ne zai kai ga wannan kamalar?

Daga nan ne zamu samu hikima ta Ubangiji ta hukumta ta sanya wa mutum abubuwan da ta hanyar su ne zai iya sani da tarbiyya da rikon hannunsa zuwa ga kamala. Yayin da abubuwan da dan Adam yake riska shi kadai da hankalinsa suka zama sun gajiya a kan su kama hannun shi wannan mutum domin su kai shi zuwa ga tafarkin tsira koda kuwa ya nemi taimakekeniya da dan’uwansa mutum, domin mafi nisan abin da dan Adam yake mallaka shi ne taimakekeniya a haddin fagen hankali da mariskai, wadanan fagage biyu ba su isa ba ga riskar hakikanin gaskiya da zata kai ga kamala.

Saboda haka ne hannun gaibi (Taimakon Ubangiji) ya miko domin toshe bukatar mutum wacce take ita ce mafi girman bukatarsa, sai mutum na farko ya zama dan aike daga Allah kuma mai shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.

Aikin annabawa ga mutane shi ne bayanin ilmi da kyawawan dabi’u da sanin gaskiya da zata kai ga kamala da tarbiyya mai kyau, da kuma bayanin ilmi da dan Adam zai iya fahimta da kuma bukatuwarsa zuwa gareshi, sai dai shi ba ya iya kai wa ga hakikaninsu ta hanyar lalatacciyar tarbiyya ko kuma mutum yana bukatar lokaci mai tsayi kafin ya kai ga gano su wadannan ilimomi, kamar sunnar Allah ta halakar da dan Adam sakamakon kaucewa gaskiya da kin ta, ko sunnar Allah akan cewa abin da mutum ya zaba da sannu zai kai shi ga sa’ada da kamala, sai dai shi ne yake barinta saboda karkatarsa zuwa ga duniya.

Sai muhimmancin aiko Annabi ya bayyana a nan domin ya tunatar, ya yi gargadi, Madaukakin sarki ya ce: “Ka tunatar domin kai mai tunatarwa ne kawai[4]”.

Kamar yadda muhimmancin Annabi ya ke bayyana da wajabcin samar da shi da la’akari da cewa shi yana misalta jagoranci ne a aiki na gari, domin shi mutum ne cikakke a ayyukansa da dabi’arsa da kuma sadaukarwarsa, wannan shi ne abin da ake cewa da shi muhimmancin tsarkake rai, madaukakin sarki yana cewa: “Yana tsarkake su yana sanar da su littafi da hikima…[5]”.

Idan hadafin halittar mutum ya zama shi ne bauta ga Allah, mutum kuma dabi’arsa an sanya masa damfaruwa da wasilar da zata kai shi zuwa ga kamala domin shi yana karkata zuwa ga kamala da sonsa na fidira, da kuma muhimmancin annabta domin bayanin hanyoyin wannan shiriya da kuma bayyana hakikanin gaskiya da takan kai zuwa ga wannan kamalar, to menene zai sa bukatar cigaba da mikuwar wannan sako ta hanyar imamanci da shi’a suke shardanta nassi a cikinta, da ilmi na baiwa daga Allah, da kuma isma?

Amsa akan wannan tambaya da waninta na daga tambayoyi yana kiranmu zuwa ga mu tambayi kawukanmu kamar haka; menenne imamanci a mahangar addinin Allah? Menene muhimmancinsa?

Bayan mun fita daga mahallin jayayya zai iya yiwuwa mu amsa wannan tambayoyi da suke zowa kwakwalwa game da imamanci da sharuddansa da suka hada da ilmi da isma da makamancinsu na daga sharudda na dole a same su ga imami.

Inda Aka Samu Sabani Yayin Bahasin Imamanci A Makarantu Biyu (Shi’a Da Sunna)

Imamanci da halifanci a makarantun sunna suna da matsayi daya da suka fuskanta da yake bayar da karfi akan cewa imami kuma halifa bayan Manzo (S.A.W) yana nufin shugaba kuma jagora na siyasa da yake tafiyar da sha’anin tsarin musulunci bayan wafatin Manzo (S.A.W).

Akan wannan asasin babu wani dalili na sanya jagora ya zama yana dogara da nassi da ayyanawa ta fusakacin Allah da kuma bayanin Manzo, al’amarin an bar shi ne ga al’umma ta zabi wanda ta so ta ga ya cancanta ga tsayuwa da wannan al’amari na jagoranci, domin muhimmancin imami kuma halifa a nazarin wannan koyarwa ba ya wuce aikin jagorancin siyasa da tafiyar da al’umma ta fuskacin haddodi, kuma yana daga abu na hankali a wannan hanya al’umma ta tsayar da halifa ya zama ta hanyar shawara (shura), ko kuma ta hanyar wakilai  (dattijan al’umma) ko ta hanyar gado.

Ya rage mu san menene sharuddan da suka wajaba ga halifa da aka zaba, haka nan zamu iya gani a wannan mahanga ta (Ahlussunna) suna ganin imamanci da halfanci bayan Manzo jagoranci ne na siyasa shi kenan, saboda haka ya isa ya zama wannan mutumin adali ne ta nahiyar aiki kamar yadda aka sani, ba a kuma shardanta masa ya zama yana da isma da ilimi da Allah ya ba shi ba, ya isa ya zama yana da iko da zai kai shi wannan matsayi a tsarin musulunci.

Sakamakon ra’ayinsu game da imamanci da halifanci shi ne ba ya wuce jagoranci na siyasa, kuma halarcin haka yana isuwa ta hanyar zabe da shura, da kwata da karfi da gado ko wasiyya, kamar yadda yake a bayyane a aikace na ayyuka masu rikitarwa da suka faru bayan wafatin Manzo (S.A.W) da sharadin adalci da ilimi daidai gwargwado.

Saboda haka ne wasu suke tambayar larurar samuwar imami boyayye ko kuma larurar ya zama ma’asumi ko larurar ayyana shi da nassi daga maznon Allah (S.A.W).

Amma koyarwar shi’a tana cewa ne imamanci da halifanci bayan Manzo (S.A.W) abu ne mai girma na Ubangiji tamkar muhimmancin aiko da Manzo, kuma mai cigaba ce har karshen duniya, sai suka shardanta isma a cikinta hatta kafin balaga, hade da ilimi da yake daga Allah, da kuma nassi na shari’a ga imami.

Saboda haka makarantar Sunna ba ta ganin wadannan sharudda da wata ma’ana da kima, kuma ba sa ganin sun dace da aikin da halifa zai yi, sharudda a nan gun mazhabin Ahlul Baiti (A.S) sun wuce na muhimmancin aikin siyasa kawai.

Wannan shi ne mataki na farko kuma wajan sabani da yake fassara mana sabanin da ake da shi a fahimtar imamanci da kuma kokwanto a mas’alar isma, ko kuma dalili na wajabcin samuwar nassi.

Wannan shi ne ya sanya wasu suka yi bincike game asalin nazarin samun nassi domin su kai ga natija zuwa ga cewa babu wani tarihin da ya nuna hakan a rayuwar imamai.

Wannan batun da aka tayar game da imamanci da halifanci da nazarin nassi da kokwanto game da hakan ya faru ne sakamkon fahimta da sunna suka yi wa imamanci.

Sai dai magana ingantacciya ita ce; imamanci a Kur’ani da sunna sun wuce wannan fahimta, kuma ta saba gaba daya daga asasinta daga irin wannan fahimta maras zurfi ta ma’anar imamanci da jagorancin al’umma bayan Annabi.

Koyarwar Ahlul Baiti (A.S) tana kudirin cewa imamai goma sha biyu suna da muhimmiyar rawar da suka taka da ta lizimta sharudda masu zurfi mafi tsanani daga sharuddan jagoranci na siyasa[6].

Alaka Tsakanin Isma Da Nassi

Idan aikin imami shi ne marja’anci na addini, kuma aikinsa a shari’ance yana mikuwa zuwa ga sasanni masu yawa da ya hada da akida, da hukuncin shari’a, da akhlaq, da jagoranci, kuma wajibi ne bin sa da karba daga gareshi, saboda haka zantuttukan imami ma’asumi da ayyukansa da kuma abin da ya tabbatar duk hujja ne na shari’a da take hawa kan baligi a wajabci da kuma uzuri ga wanda bai sani ba daidai da hujjar ayyukan Manzo (S.A.W).

Wanan aiki mai girma yana lizimtar abubuwa da yawa kamar haka; Imami ya zama ma’asumi kamar ismar Manzo da kuma wajabci kansa na isar da sako da kuma aiki, wanan yana bayyana cewa isma da wannan ma’ana ba sharadi ba ce ga aikin jagoranci na siyasa kadai.

Muhimmancin aikin imamanci ya wajabta imami ya zama masani da dukkan abin da al’umma take bukata zuwa gareshi na rayuwarta da makomarta, kuma dole ya zama mafifici daga duk wanda yake bayan kasa a zamaninsa domin ya samu bayar da hakkin wannan aiki mai nauyi.

Shi’a suna da imani cewa Manzo (S.A.W) ba shi da kansa ne ya ayyana halifa ba, a’a al’amari ne da Allah ya umarce shi da shi, domin hadafin imamanci da kuma al’amarinta ya ta’allaka da al’amarin cikar annabta da kuma cigaban shiriya ta Ubangiji akan layi daya.

Hikimar Allah ta sanya cigaban isar da sakon Allah ya zama ta hanyar ayyana imami ma’asumi, imami shi ne wanda ya lamunce samar da maslaha ta tilas ga al’ummar musulmi bayan Manzo (S.A.W).

Ashe kenan matsayin imamanci na akida ba kamar fikihu ba ne na daga hukuncin rassa, wannan shi ne abin da ya sanya imamanci ya zama yana da wadannan sharudda masu fadi masu girma, kuma ya wuce matsayin jagoranci na siyasa kadai.

 Idan muhimmancin imamanci yana da fadin da ya wuce jagorancin siyasa to dole ne ya zama yana da sharadi da zai tilasta gaskatawa da ita a matsayin wani asasi na addini kai tsaye saboda abin da yake mai girma na sakon da take dauke da shi.

Shahidus sani a risalarsa: Asasi na hudu shi ne gaskatawa da imamancin imamai sha biyu (A.S), wannan asasi jama’ar imamiyya su na la’akari da shi wajan tabbatar imani, har ma ya zama wani larura daga larurai na mazhabarsu sabanin wasunsu na daga masu saba musu, su sun dauki wannan a matsayin furu’a ne[7].

Saboda haka ne zamu samu cewa ala’amarin ayyana imamai yana wajen hakkin dan Adam ne, kuma ba zai iya zabar wanda yake da isma ba ko kuma ya gano wanda yake da ilmi na baiwa daga Allah da sauran siffofin da imamai (A.S) suke dauke da su.

Rashin kasanewar zabin imamai ta hanyar dan Adam ya yi kama da zabin annabawa da Allah yake zabar wanda ya so kuma a gane hakan ta hanyar wahayi da nassi. Bambanci tsakanin Annabi da imami shi ne Allah yana nuna Annabi ta hanyar mu’ujiza da wahayi, imamai kuma ta hanyar mu’ujiza da nassi.

Sharif Murtada yana fadi a risalarsa cikin abin da yake wajibi a kudurce shi game da annabta: Duk sadda Allah madaukakin sarki ya san akwai maslaha a cikin wasu daga ayyukanmu da tausasawarsa, ko kuma akwai fasadi da barna na addini a ciki, kuma hankali ba ya iya gano ta, wajibi ne ya aiko Annabi domin ya sanar da wannan ga mutane, kuma babu wata hanyar gano shi sai da mu’ujiza. Mu’ujiza kuma dole ta kasance ta saba wa al’ada, kuma ta yi daidai da da’awar Manzo din da abin da ya shafi da’awarsa, ta kuma kasance ba za a iya zuwa da ita ba ta bangaren wani mutum, kuma aikin ya zama ya yi daidai da yadda Allah (S.W.T) ya gudanar da shi, idan wannan duk ya faru to wajibi ne a gaskata shi, in ba haka ba to sai rashin gaskata shi ya zamanto ya munana.

Daga abin da ya zo a babin abin da ya wajaba a kudurce shi a imamanci da kuma abin da ya biyo bayansa ya wajabta kasancewar imami ya zama ma’asumi, domin da bai zama hakan ba, da bukatuwa a gareshi ba ta kare ba, wannan kuma yana tukewa zuwa ga samar da shugaba ma’asumi, kuma wajibi ne ya zama mafificin al’umarsa mafi saninta, saboda munin gabatar da wanda aka fi akan wanda ya fi shi a hankalce, Idan ya wajaba ya zama ma’asumi to wajibi ne a samu nassi daga Allah akan hakan, kuma zabar imamanci ta bangaren mutane ya kawu kenan, domin babu wata hanya da mutane zasu iya sanin mai isma[8])

Don haka ne zamu samu nassi da yake daya daga rukunan isma a mahangar shi’a da yake nuna ajiya ta Ubangiji da take tattare da wannan imami, daga nan ne zamu sami cewa nassi shi ne mai kai wa ga sanin halifa mai bin Manzo (S.A.W) a wannan aiki na addini da ci gabansa.

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com

[1] - Muminun: 115.

[2] - Dukhan: 38.

[3] - Zariyati: 56.

[4] - Gashiyat: 21.

[5] - Jumu’ati: 2.

[6] - koma wa bahasin kamal haidari game da imamanci.

[7] - aka’idul islmiyya: 1\282 markazul mustapha, daga rasa’il na shahidussani:2\145,

[8] - Aka’idul Islmiyya: 1\281 Markazul Mustapha, Da Rasa’il Na Sharif Murtada:3\18.