Ahlul Baiti (A.S) a cikin Kur’ani mai girma:
“Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya kuma tsarkake ku tsarkakewa”
Surar Ahzab\ aya: 33
Ahlul Baiti (A.S) a cikin hadisai madaukaka:
“Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su”
Sahihan Littattafai Da Masanid
Bai’a girmamawa ce ga mutum domin ya zabi makomarsa a cikin kira zuwa ga Allah da jihadi a tafarkinsa ko sha’anin hukunci da siyasa.
muslunci a bisa dabi’a ba ya son rayuwar musulmi ta kasance ba tare da nufinsu ba da kuma yardarsu ba. Biyayya a nan ita ce mafi muhimmnaci a cikin zartar da ayyukan isar da sako da kira, da kuma ayyukan kasa, da jihadi, da karfafa wa ga bin imamai ma’asumai ta hanyar bai’a. Amma wannan ba yana nufin biyayya ga imami ma’asumi tana saraya ba ne idan ba a yi masa bai’a ba.
Idan bai’a ta kasance to tana karfafa imami da biyayya gareshi ne, bayan an tabbatar da samuwarsa. Shin zai iya yiwuwa garemu mu ce: bai’a sharadi ce ta inagancin biyayya ga imam, ko kuma sharadi ce ta wajabcin biyayya gareshi ta yadda zai zama idan babu bai’a ba shi da imamanci, ko kuma babu inganci ga binsa?
Sai mu ce: Bai’a tana karfafa dankon wajabcin lizimtar wilayarsa da biyayya ga jagoracinsa ne ba tana kafa ko samar da assassin asalin wilayar ba ne ko kuma ta zama sharadi na inagncin biyayya gareshi, domin biyayya da imamanci ba sun tsayu ba ne akan bai’a ga wanda wilaya ta tabbata gareshi da nassi.
Shi ya sa zamu samu cewa, Manzo (S.A.W) ya yi aiki da bai’a a lokacin rayuwarsa kamar yadda yake a fili a bai’ar Akaba ta farko da bai’ar Akaba ta biyu da bai’ar Gadir.
Wannan sura ta bai’a da ta faru ga Manzo (S.A.W) tare da cewa wilaya ta tabbata gareshi tun kafin wannan bai’a din, Bai’ar da musulmi sukan yi masa ko rashin bai’ar su gareshi (S.A.W) a game da amsa kiransa ko jihadi ko shugabanci, ba ya canza hakkin Manzo akan al’umma na biyayya ga al’amarin kira da jihadi da jagoranci.
Haka nan shugabancin imam Ali (A.S) bayan Manzo (S.A.W) da ya tabbata a Gadir, Bai’ar da musulmi suka yi masa a rannan ba ita ce zata tabbatar masa da shugabanci ba ta fuskacin sharia’a duk da Manzo ne ya umarce su da su yi masa tun yana raye, ita wannan bai’ar ba ta kara kimar wilayarsa ta nahiyar shari’a akan karfafa wilaya da biyayya, Kuma kasancewar imamanci (jagoranci) yana samuwa ne ta hanyar wasiyya da dama daga malaman Ahlussunna sun tafi akan haka.
Suka ce: Idan wani halifa ya yi wasiyya zuwa ga wani bayansa to bai’ar sa ta kullu domin yardar al’umma da ita ba a la’akari da ita, dalilin haka shi ne bai’ar Abubakar ga Umar ba ta tsayu akan yardar sahabbai ba[1].
Wannan kenan, tare da cewa ba mu samu bai’a ba tsakanin Abubakar da Umar, abin da ya faru kawai ya yi wasiyya da halifanci ne kawai ba wani abu ba.
Idan haka ne wanda Annabi ya yi wasiyya gareshi shi ya fi cancanta a bi ba tare da wani dalili ba akan sabawa hakan, kuma al’amarinsa zartacce ne, kuma da wannan ne halifanci ya tabbata ga Ali (A.S) bayan Manzo (S.A.W) kai tsaye shin ko al’umma ta yi masa bai’a akan biyayya ko ba ta yi ba, bai’a tana kasancewa ne daga alkawarin biyayya da karbar tafiyar da hukunci da tafiyar da al’amuran al’umma; wannan kuma ba ya yiwuwa sai da bai’a, kuma Abbas ya halartowa Ali da ita sai yaki karba sai dai a fili a gaban mutane a masallacin Annabi madaukaki, sannan da aka zo yin bai’a akan hakan ne mutane suka yi masa bai’a, haka nan al’amarin ya kasance game da Imam Hasan (A.S), shi ya sa yayin da sauran imamai da Allah ya zabe su ga jagorancin al’umma ya zama ba a yi musu bai’a ba sai aka kange su gabarin tafiyar da hukuma da al’amuran al’umma, amma kuma wannan ba ya cire musu hakkinsu na imamanci ba ne garsu, sha’anin al’amarinsu yana daidai da na annabawa ne da al’ummarsu suka saba musu suka hana su tafiyar da jagoranci da shiryarwa da fuskantarwa, ba tare da wannan ya cire musu matsayinsu da Allah ya ba su ba[2].
Ashe kenan matsayin bai’a a lokacin halartar imami ma’asumi ba komai ba ne sai karfafawa ga wanda jagoranci ya tabbata gareshi ta hanyar nassi. Kamar yadda bai’a ba ta iya samar da wilaya ga mutum da aka yi nassin binsa kamar Manzo ko imami, nassi ga imami yana wajabta binsa da haramcin rashin yi masa bai’a.
Idan muka kula da nazari ta fuskancin tarihi muka kuma lura da matakan da Annabi ya dauka wajan tarbiyyar al’umma da wayar da ita game da al’amarin Ubangiji wanda ya shafi halifanci sai mu samu cewa ya karfafa nazarin nassi a kwakwalenmu ne ba shura ba, kuma ba a samu wani waje da Manzo ya ambaci wayar da al’umma da tarbiyyantar da ita akan nazarin shura ba tun daga saukar fadin Allah madaukaki “Ka gargadi jama’arka makusanta”. Har zuwa saukar fadinsa madaukakin sarki: “Ya kai wannna Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga ubangijinka, idan ba ka aikata ba to ba ka isar da sakonsa ba kuma Allah yana kare ka daga mutane”.
Hakika ya zo daga dan Abbas daga imam Ali (A.S) cewa ya ce: “Yayin da wannan aya ta sauka; “Ka gargadi jama’arka makusanta” ga manzon Allah (S.A.W) sai ya kira ni ya ce: Ya Ali Allah ya umarce ni da in gargadi jama’ata makusanta, sai na samu kunci na san cewa idan na bayyana wannan al’amari to zan ga abin ki daga garesu, sai na kame gabarinsa sai Jibril ya zo mini, ya ce: Ya Muhammad idan ba ka yi abin da Allah ya umarce ka to zai azabtar da kai, saboda haka ka yi mana abinci sa’i daya ka kuma sanya karfatar akuya ka cika mana kwano na nono, sannan ka kira duk Bani Abdulmudallib domin in yi musu magana in isar musu da sakon da aka umarce ni da shi, sai na aikata abin da ya umarce ni da shi sannan na kirasu su a wannan lokaci mutum arba’in ne da daya ko ba daya, a cikinsu akwai ammominsa abu Talib da Hamza da Abbas da Abu Lahab, Ya ce: Sai manzon Allah (S.A.W) ya yi magana ya ce ya Bani Abdul Mudallib ni wallahi ban san wani saurayi a larabawa da ya zo wa mutanensa da mafifici daga abin da na zo muku da shi ba, ku sani ni na zo muku da alherin duniya da lahira kuma hakika Ubangiji ya umarce ni da in kira ku zuwa gareshi, wanene a cikinku zai karfafe ni akan wannan al’amari akan ya kasance dan’uwana wasiyyina kuma halifata a cikinku?, Imam Ali ya ce: Sai duk mutanen suka tage gaba daya sai na ce alhalin ni ne na fi kowa karancin shekaru a cikinsu, ni ne ya Annabin Allah zan zama mai taimakon ka akansa, Sai ya riki kafadata sannan ya ce: Wannan shi ne dan’uwana kuma wasiyyina halifata a cikinku ku ji ku bi daga gareshi, Ali (A.S) ya ce: Sai mutanen suka tashi suna dariya suna cewa da Abi Talib ya umarce ka ka ji daga danka kuma ka bi shi”[3].
Haka nan Manzo Allah (S.A.W) ya fara shirya wa al’umma tun daga farawa da makusantansa yana mai nuna wa al’umma halifancin Ali (A.S) bayansa, yana mai wasiyya akan dan’uwansa da wasiyya da halifanci da kuma wajabta biyayya gareshi, Annabi ya kasance yana mai bayyyan ma’anar ayoyin Kur’ani da suke sauka akansa game da hakkin Ali musamman ayoyin da suka shafi halifanci da imamanci.
Zamakhshari a tafsirinsa yana fada game da fadin Allah (S.W.T): “Kadai shugabanku Allah ne da manzonsa da wadanda suka yi imani wadannan da suke tsaida salla suke bayar da zakka alhalin suna masu ruku’i”[4], Wannan aya ta sauka game da imam Ali (A.S) yayin da wani ya tambaye shi yana mai ruku’u a cikin salla sai ya jefa masa zobensa[5].
Domin kawar da rikitarwa da kuma yanke duk wani tawili game da abin da ake nufi da kalmar wali da kuma nuna ko waye a wannan waje sai Annabi (S.A.W) ya bayyana a wajaje da dama cewa: “Ali daga gareni ne, ni ma daga gareshi nake, kuma shi ne shugaban duk wani mumini bayana”[6].
Saboda karfafa shuganbacin imam Ali (A.S) da kuma matsayinsa mai muhimmanci a wajan bayyana sakon musulunci da kuma cimma hadafofin ta hanyar aiwatar da jagoranci domin dabbaka hukunce-hukunce da kuma kare su daga dukkan abind zai iya karkatar da su da kuma canja su bayan Manzo sai Annabi (S.A.W) ya ce: “Ali daga gareni yake ni ma daga Ali nake, kuma ba mai bayar wa daga gareni sai ni ko Ali”[7].
Kuma Manzo (S.A.W) ya karfafa wannan ma’ana a aikace a bayyane da rana a kissar isar da sako a surar bara’a, kuma imam Ahmad dan Hanbal ya fitar da wanan ruwaya a musnadinsa daga Abubakar yayin da ya ce: “Annabi ya aika ni da bara’a zuwa mutanen Makka, sai ya tafi kwana uku sannan sai ya ce da Ali: Ka yi maza ka riske shi, sai Abubakar ya mayar da ita gareni na isar da ita, yayin da Abubakar ya zo wajan Manzo (S.A.W) sai ya ce: Ya manzon Allah shin wani abu ne ya faru game da ni?! Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ba komai game da kai sai alheri, sai dai ni an umarce ni da kada wani ya isar da sako daga gareni sai ni ko wani mutum daga gareni…[8].
A littafin Kusshaf: Abubakar ya rawaito cewa: Yayin da yake kan hanya domin isar da surar bara’a sai Jibril (A.S) ya sauka ya ce: “Ya Muhammad kada wani ya isar da sakonka sai wani mutum daga gareka, sai ya aika Ali…”[9].
Daga karshe Kur’ani ya cika wannan maudu’i mai muhimmanci wanda ya shafi haifar da tunani da tarbiyyantarwa akan yadda al’amarin shugabanci da halifanci zai kasance bayan Manzo (S.A.W) a karshen abin da ya sauka garshi a ayar tablig sannan da kuma ayar cika addini bayan kissar Gadir mash’huriya ta yadda babu wani uzuri ga mai kawo uzuri, Kissar Gadir kissa ce da dayawa sun rawaito ta da dan sabani kadan a wasu wurare Kamar yadda zai zo:
Yayin da Manzo (S.A.W) ya dawo daga hajjin bankwana, sai wahayi ya sauka akansa yana mai tsananta masa: “Ya kai wannan Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga ubangijinka idan ba ka aikata ba to ba ka isar da sakonsa ba kuma Allah ne yake kare ka daga mutane”[10], sai ya tsayar da jama’a gun Gadir khum, ya tara mutane a tsakiyar rana, ga zafi mai tsanani, ya yi musu huduba yana mai cewa: “An kusa kira na sai in amsa kuma ni mai bar muku sakalaini ne, daya ya fi daya girma, littafin Allah da zuriyata, a ruwayar Muslim[11] da Ahlin gidana ku duba yadda zaku maye mini a cikinsu, domin su ba zasu rabu ba har sai sun riske ni a tafki…” sannan sai ya ce: “Hakika Allah shugabana ne kuma ni shugaban duk wani mumini ne”. Sannan sai ya kama hannun Ali ya ce: “Duk wanda nake shugabansa to wannan shugabansa ne -ko wannan majibancin lamarinsa ne[12]- ya Ubangiji ka so wanda ya so shi ka ki wanda ya ki shi, ka tozarta wanda ya tozarta shi, ka taimaki wanda ya taimake shi[13],, ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya…”[14].
Kuma hakika saukar wahayi da wannan aya ya biyo bayan faruwar wannan abu mai girma da fadin Allah (S.W.T): “A yau ne na kammala muku addininku na kuma cika ni’imata a gareku na yardar muku da musulunci shi ne addini”[15],
Wasu hadisai da aka rawaito daga Manzo (S.A.W) sun cewa, bayan saukar wannan aya a wannan rana abar halarta wanda ita ce ranar sha takwas ga watan zil-hajji[16] ranar Gadir sai ya ce: “Allah mai girma! Godiya ta tabbata ga Allah akan kamala addini da cika ni’ima da yardar Ubangiji da manzancina da kuma shugabancin Ali bayana”[17].
A ruwayar Ahmad: “sai Umar dan khaddabi ya gamu da shi –imam Ali- bayan nan, sai ya ce da shi: Farin ciki ya tabbata gareka ka wayi gari ka maraita shugaban dukkan mumini da mumina…”[18].
Ba mu samu wani abu ba a rayuwar Manzo (S.A.W) da yake ambaton wani abu da zai iya tabbatar da cewa Manzo ya nufi tabbatar da al’amarin halifanci bayansa in banda nazarin wasiyya a matsayinta na sakon shari’a ba a matsayin jagoranci na siyasa ba kawai, shi al’amari ne da yake Ubangiji ne da yake aiwatar da zabar abin da ya so na sakon manzancin Annabi (S.A.W) yayin da Kur’ani ya yi nassi akan Annabi da cewar idan bai isar da wannan al’amari wanda ya isar ba -na sakon halifanci da shugabanci bayansa- da bai isar da komai na sakon da ya dauki shekara ishirin yana wahala a kan isar da shi ba[19].
Shahid Sadar (Q.S) ya yi munakashar wannan mas’alar da ta faru a tarihi da bayanai kamar haka;
Daga ciki: Tsammanin cewa Manzo (S.A.W) ya riki wata hanya ta barin mutane ba magaji ba halifa, da ma’anar cewa Manzo bai taba tarbiyyantar da mutane akan al’amarin halifanci ba da jagoranci bayansa, wannan kuma batacce ne domin ya yi karo da matasyin Annabi wanda yake sane da dukkan makomar sakon da ya zo da shi, sannan ya ci karo da hadisai da suka yi Magana game da muhimmancin al’amarin al’umma bayansa a rayuwarsa da kuma kafin wafatinsa a karshen rayuwarsa[20].
Kamar yaddda shahid Sadar ya yi soke ra’ayi na biyu wanda yake ganin shura da fadinsa: Abin da aka samu daga Manzo gaba da daga muhajirai da Ansar ya kore batun shura.
Domin da Annabi ya dangana ala’amari zuwa ga hannun Muhajirun da Ansar bai tasakace shi da Ahlin gidansa (A.S) ba, da wannan al’amari ya zama daga mafi bayyanar al’amura da kuma ya wayar da kan al’mmma akan tsarin shura da bayaninsa dalla-dalla domin mutane su san yadda tsarinta yake.
Da Annabi (S.A.W) ya wayar da su akan haka to da kuma an samu bayyanar wannan a cikin hadisansa da suke rawaitowa daga gareshi da take dauke da bayani game da shura. Amma sai ya zama ba mu samu wani wanda yake dauke da wannan tunani ba, sai ya zama al’ummar Muhajirun da Ansar duka mun same su ne jama’a guda biyu mabanbanta.
Na daya: Jama’ar da Ahlul Baiti suke jagoranta mai dauke da tunanin wasiyya da Manzo (S.A.W) ya yi game da halifancinsu,
Na biyu: jama’ar mutanen Sakifa da suke bin halifanci da ya biyo bayan wafatin Manzo (S.A.W).
Kuma a dukkaninsu ba wanda yake dauke da tunanin shura kamar yadda tarihi ya nuna, yayin da Abubakar ya yi wasiyya da halifancin Umar bai nemi shawarar kowa ba sai ya dora shi kan halifanci akan al’umma ba tare da shawarar musulmi ba, ko shugabanninsu, sai Umar shi ma ya tafi akan wannan tafarki ya zabu wasu wadanda zasu zabi wani daga cikinsu, ya kasance yana cewa: “Da Salim ya kasance rayayye da ban sanya ta shura ba”, Wannan kuma bayani ne karara daga gareshi da rashin imaninsa da shura[21].
Da Annabi ya dauki matakin ya sanya ta shura a tsakanin mutane da ya sanya wannan a da’awarsa tun farko domin ya sanar da wannan al’umma al’amarin sakon Allah da zai iya ba ta damar fuskantar duk wata matsala ta tunani da fikira da wannan kira zai iya fuskanta, yayin da ake samun karuwar budi da shigowar al’ummu jama’a daban-daban.
Sai ya zama ba mu samu komai ba dangane da wannan, kuma abin da aka sani daga sahabbai sun kasance suna jin nauyin fara tambayar Manzo (S.A.W), kai har ma sun bar rubuta sunnar Manzo (S.A.W) duk da kuwa ita ce madogara ta biyu ta shari’a bayan Kur’ani, tare da cewa rubutawa ita kadai ce hanyar da ta rage domin kiyaye ta.
Kuma tarihi ya tabbatar da cewa ‘ya’yan Muhajirun da Ansar ba su da komai a hannunsu na daga abin da ya shafi ilimi game da mas’aloli masu yawa, sai ga shi hatta da kasar da ake ci yaki halifa ba shi da wani hukumci na shari’a game da ita a hannunsa da ya sani, ko a raba ta tsakanin mayaka ko ta zama wakafi ga dukkan musulmi, Kai har ma sun yi sabani akan yawan kabbarorin sallar mamaci, wasu suna cewa Manzo ya yi biyar, wasu suna cewa ya yi hudu ne.
Haka nan ya bayyyana a fili cewa Manzo bai kawo shura ba, sai ya zama ba abin da ya rage sai hanya ta uku wacce take cewa Manzo (S.A.W) ya shirya imam Ali da umarinin Allah ya kuma sanya shi halifansa akan sako da al’umma bayansa a matsayinsa na mai masaniya da zurfin abin da wannan sako ya kunsa da kuma iko akan kula da tafiyar sakon da cigabansa bayan Manzo (S.A.W), kamar yadda ya tabbata a tarihi a shekaru talatin da ya yi bayan wafatin Manzo (S.A.W) da furucin masu tarihi.
Kuma duk abin da da ya zo na hadisai mutawatirai game da Ahlul Baiti (A.S) ba komai ba ne sai karfafa wa ga wannan hanya ta uku, wato ayyana halifansa da umarnin Allah (S.W.T)[22].
[1] - Ma’asirul Anafa: 1\52, Da Ahkamussuldaniyya Na Mawardi: 10, Da Ahkamussuldaniyya Na Farra’u: 25, 26.
[2] - Tarihul Islmi Assakafi Was Siyasi Na Sa’ib Abdulhamid: 259-260.
[3] - Tarihi Tabari: 3\218-219, Mausu’atut Tarihil Islami: 1\407-427, da Ma Nazala Minal Kur’ani Fi Ali Na Abu Na’im: 155, Da Tafsirul Khazin: 3\371.
[4] - Ma’ida: 55.
[5] - Alkusshaf Na Zamakhshari: 1\649.
[6] - Sunan Tirmizi: 5\591, Babu Fada’ilil Imam Ali, Da Tajul Jami’i Lil Usul: 3\335.
[7] - Sunan Tirmizi: 5\594, Babu Fada’ilil Imam Ali, Da Tajul Jami’i Lil Usul: 3\335.
[8] - Masnad Ahmad Bn Hanbal: 1\3, Da Sunan Tirmizi: 5\593, Da Tafsirul Khusshaf, Na Zamakhshari: 2\243.
[9] - Kusshaf: 2\243.
[10] - Ma’ida: 67.
[11] - Sahih Muslim: 4\1874.
[12] - Sunan Tirmizi: 5\591, Da Tajul Usul: 3\333.
[13] - Masnad Ahmad: 4\281, 368, Da Ibn Kasir: 1\22, Da Bidaya Wannihaya Na Ibn Kasir: 7\360-361.
[14] - Taju Jami’ul Usul: 3\337.
[15] - Ma’ida3.
[16] - Itkan Na Suyudi: 1\75.
[17] - Manakubu Amirulmuminin, Na Muhammad Sulaiman Kufi Alkadi: 1\119.
[18] - Masnad Ahmad: 4\281, Da Bidaya Wannihaya Na Ibn Kasir: 7\360.
[19] - Wannan ya isa ya nuna muhimmancin wannan sako.
[20] - Komawa Yaumuddari, da Inzaril ashira, da matsayinsa a tabuka, da surar bara’a, da Raziyyar ranar alhamis lokacin da Annabi ya so ya rubuta wasi- yyarsa a Buhari da sauran littattafai.
[21] - Tarihi Tabari: 3\292.
[22] - Nash’atus Tashayyu’u Wasshi’a: 63, 64.