DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI  JINKAI

TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA MANZON RAHAMA

DA ALAYENSA TSARKAKA

Ahlul Baiti (A.S) a cikin Kur’ani mai girma:

 “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya kuma tsarkake ku tsarkakewa”

Surar Ahzab\ aya: 33

Ahlul Baiti (A.S) a cikin hadisai madaukaka:

 “Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su”

Sahihan Littattafai Da Masanid

Game Da Bai’ar Imam Ali (A.S) Ga Halifofi Uku

Sun kawo matsalar cewa imam Ali (A.S) ya yi wa halifofi uku bai’a, suka raya cewa wannan bai’ar kuma ba zai yiwu a ce domin maslaha ya yi ta ba, ko domin takiyya, ko tilastawa, domin wannan yana nuna tauye matsayi na imam Ali (A.S).  Amsar da zamu bayar ita ce: Game da tilasta shi wanan abu ne a fili, da masu tarihi suka rawaito.

Buhari yana cewa: “Ali (A.S) ya ki yin bai’a ga Abubakar tsayin wata shida har sai da Fadima (A.S) ta rasu”[1]. A hudubar imam Ali (A.S) ya fadi dalilin da ya sa ya yi bai’a a hudubarsa da yake cewa:

A- “Na rantse da Allah ba domin tsoron rarraba ba, kafirci ya dawo addini ya rushe, da mun kawar da wannan jagoranci, amma sai muka yi hakuri akan wasu zogi da bakin ciki da yake damun mu”[2].

B- Yana fada a Nahajul Balaga: “Sai na duba, sai ga shi ba ni da wasu masu taimaka mini sai Ahlin gidana (A.S) sai na yi wa mutuwa rowarsu, na kuma runtse idanuna akan wannan kwantsa, na yi himmar hadiyar bakin ciki, na yi hakuri akan juriya da kuma hakurin dacin da ya fi na madaci”[3].

Shin zai yiwu a zo da wani bayani wanda ya fi wannan zama karara?! In ba haka ba menene ya sa duk wannan bayan irin wannan kukowa da kai kara? Alhalin shi ne mafi sanin mutane da halin da ake ciki da sakamakon abin da ya faru.

Da a ce bai kafa musu hujja ba ya baro janazar Manzo (S.A.W) ya tafi Sakifa ya bar jikin masoyinsa (S.A.W) bai wanke shi ba, ya zo ya dora hannunsa akan hannunsu ya yi bai’a da ba ma’ana ya zo da irin wannan kafa hujja. Idan ya tabbata ta hanya sahihiya Ali dan Abi Talib (A.S) cewa ya soki nazarin shura ya kuma shelanta cewa ta saba wa shiri’a… ya kuma fadi cewa an tilasta shi ne ya yi bai’a ga halifofi uku to bai’arsa ba ta da wani dalili na shari’a akan halifancinsu kamar yadda wannan ya tabbata a fili daga maganganunsa.

Sannan ya bayyana cewa shi ne ya fi cancanta da halifanci, shin zai yiwu mu ce cancantarsa ga halifanci tana nufin shi ya fi da ma’anar cewa waninsa ba komai ko kuma tana nufin shi ne kadai ya cancanta da halifanci?.

Wannan ra’ayi na farko ba daidai ba ne saboda nassin hadisai da kuma maganganun imam Ali (A.S) yayin da ya ke cewa: “Mutane sun yi bai’a ga Abubakar alhalin ni ne na cancanci  in -sanya- rigata wannan daga garesu”. Wannan yana nufin cancantar da ta kebanta da shi, ba wai yana nufin fifikon cancanta ba ta yadda wani ma yana iya cancanta da ita, domin ba ma’anar ya ce rigarsa ce sannan ya zama ba ya nufin cancanta, domin mai riga shi ne mai ita mai cancanta da ita mai mallakarta.

Sannan ga fadinsa da yake cewa: “…Na zama ina mai kai-kawon ko ina tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu, da babba yake tsufa a cikinsa yaro kuma yake girma a ciki, mumini yake shan bakar wahala aciki har sai ya riski ubangijinsa.

 Sai na ga hakuri akan wannan ya fi lizimtuwa, sai na yi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kuma shakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa”[4].

Ma’anarsa sai na samu kaina tsakanin ko in karba da karfin da bai isa ba kamar yadda ya zo a fadarsa (A.S): “Sai na duba, sai ga shi ba ni da wasu masu taimaka mini sai Ahlin gidana (A.S) sai na yi wa mutuwa rowarsu”. Wato da ya sami karfi isasshe da ya yaki ma’abota Sakifa kamar yadda yake a maganarsa da aka sani da yake cewa: “Da na samu mutum arba’in masu niyya da gaskiya da na kawar da mutunen”.

Wannan mataki na imam Ali (A.S) ba yadda za a fassara shi da ma’anar ya fi cancanta da ma’anar wani ma yana iya rikon jagoranci, wannan a fili ya ke cewa ya yi daidai da ma’ana ce ta cancantar kebantaka da shi. Hakanan fadinsa (A.S): “Ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu…”. Ma’anarsa abin da ya faru ba kawai kwacen mulki ba ne, a’a wannan yana zama farkon faruwar canji ne da zai iya kai al’umma ga bata, Shi ya sa ya karfafa wa mutane bayan kashe Usman dan Affan yayin da suka zo domin yi masa bai’a: “ku rabu da ni ku nemi wanina domin tafarki ya bice hujja kuma an yi musun ta”[5], da fadinsa garesu: “Ni ina ji muku tsoro ne ku kasance cikin wani yanayi na lokaci, alhalin da can wadansu al’amura sun faru sun wuce da kuka karkata zuwa garesu karkatar da kuka zamo ba abin yabo ba ne ku a guna”[6].

Dalilan Tarihi Akan Ingancin Mahangar Nassi

Dalilan tarihi a rayuwar Annabi (S.A.W) da Ali akan cewa Manzo (S.A.W) ya kasance yana yana shiryar da Ali da tarbiyya na daukar sako bayan wucewarsa, yana ba shi ilimi da tunani yana kuma kebewa da shi kowane dare da rana, yana wayar da shi akan abin da sakon musulunci yake dauke da shi da matsalolin tafarkin har zuwa ranar karshe ta rayuwarsa.

Nisa’i[7] ya rawaito da sanadinsa zuwa ga Abi Ishaq, ya ce: An tambayi kusum dan Abbas cewa, yaya Ali ya zama mai gadon Annabi (S.A.W) banda ku? Sai ya ce: Domin shi ne na farkon haduwa da shi kuma mafi damfaruwa da shi”.

Haka nan ya rawaito[8] daga Ali (A.S) ya ce: “Na kasance idan na tambaya sai a ba ni, idan na yi shiru sai a fara –gaya- mini”.

Abu Na’im ya rawaito a littafin Hilyatul auliya daga dan Abbas ya ce: “Mun kasance muna magana a lokacin Annabi (S.A.W) cewa ya ba wa Ali wasiyya (ilimi) saba’in da bai ba wani shi ba”[9].

Nisa’i ya rawaito daga Ali (A.S) ya ce: “Ina da wani matsayi gun manzon Allah (S.A.W) da babu wani makhaluki da yake da shi, na kasance ina zo masa kowane karshen dare sai in ce: Assalamu alaika ya nabiyyallah, idan ya yi gyaran murya sai in koma zuwa ga Ahlina, in ba haka ba sai in shiga wajansa”[10].

Daga gareshi ya ce: “Ina da shiga guda biyu wajan manzon Allah, daya da dare, daya da rana”[11].

Wannan irin tarbiyyantarwa ga Ali da Manzo (S.A.W) ya yi masa ya yi tasirin da Ali ya zama shi ne madogarar kowa makoma ga warware duk wata matsala da aka kasa warware ta hatta da masu jagoranci a wannan lokaci, amma ba a taba samun wata matsala guda daya ba a tarihin imam Ali da ya koma zuwa ga wani mutum ko daya, yayin da a tarihi akwai mas’aloli da dama da dukkkan halifofi suka koma zuwa gareshi duk da kokarin boye wannan matsayi nasa da aka yi.

Amma tarihi ya riga ya tabbatar mana shelantawar da Annabi (S.A.W) ya yi game da hikimar da yake da ita wajan ba wa Ali tarbiyya da ilimi na musamman wanda suna da yawa da suka faru a lokuta daban-daban, kamar hadisuddar, da hadisin sakalaini, hadisin manzila, da hadisin Gadir, da gomomin hadisai[12].

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com

[1] - Sahihul Buhari: 5\288 Da Tarihin Tabari: 2\234.

[2] - Nahajussa’ada: 1\248 Na Shaikh Mahmudi.

[3] - Nahajul Balaga, Dr Subhi Salih: 68, Huduba 26.

[4] - Biharul Anwar: 28\313, Daga Ibn Abil Hadid: 10\151.

[5] - Nahajul Balaga, Dr Subhi Salih: 136, Huduba 92.

[6] - Nahajul Balaga, Dr Subhi Salih: 2\256, Huduba 178, da Shubahtun wa Rudud: 3\47.

[7] - Alkhasa’is: 91, Da Mustadrik Na Hakim: 3\136.

[8] - Alkhasa’is: 98, Da Mustadrik Na Hakim: 3\135.

[9] - Hilyatul Auliya: 1\68.

[10] - Alkhasa’is: 97.

[11] - Alkhasa’is: 96.

[12] - Sahih Tirmizi: 5\297, Sunan Ibn Majah: 1\44, Hilyatul Auliya: 1\63. Shawahiduttanzil; 1\161.