DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI  JINKAI

TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA MANZON RAHAMA

DA ALAYENSA TSARKAKA

Ahlul Baiti (A.S) a cikin Kur’ani mai girma:

 “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya kuma tsarkake ku tsarkakewa”

Surar Ahzab\ aya: 33

Ahlul Baiti (A.S) a cikin hadisai madaukaka:

 “Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su”

Sahihan Littattafai Da Masanid

Dalilin Tabbatar Wasiyya Daga Ruwayoyi

Idan nazarin samuwar nassi ya tabbata ita ce kadai hanyar shari’a da Annabi (S.A.W) ya tabbatar da ita a rayuwarsa a tarihi. Kuma imam Ali (A.S) ya ki dukkan wani abu da zai zama makoma ga jagoranci bayan Manzo in ba wasiyya ba, sai ya rage mana mu yi bincike game da dalili ta fuskacin shari’a da yake tabbatar da cewa Manzo (S.A.W) ya yi wasiyya da imam Ali (A.S) da halifanci bayansa, kamar yadda shi ma ya yi wasiyya da halifanci da imamai bayansa.

Shi’a suna da akidar cewa imamancin imam Ali da ‘ya’yansa Hasan da Husain da kuma tara daga zuriyar Husain (A.S) duk an samu nassi da ya zo game da hakan daga manzon Allah (S.A.W) wanda kuma kowanne daga cikinsu ya yi wasiyya da mai bi masa, nassosin hadisan sun kasu gida uku ne:

Nau’i na farko: Abin da yake wajabta komawa zuwa ga Ahlul Bait (A.S) ba tare ya fadi sunayensu ba; kamar hadisin sakalaini da hadisin safina wadanda mutawatirai ne daga Shi’a da Sunna.

Nau’i na biu: Abin da yake iyakance adadin halifofin Annabi da cewa sha biyu ne kuma daga kuraishawa daga Bani Hashim suke, Wannan kuma adadi ba ya dabbakuwa sai a kan imamai na Ahlul Baiti (A.S), sabanin idan an dabbaka shi akan wasunsu.

Nau’i na uku; Hadisan da suka zo da ambaton sunayensu (A.S) har guda goma sha biyu, ta hanyar Shi’a da Sunna.

Amma Abin da Ya Zo A Nau’i Na Farko

Tirmizi ya rawaito daga Jabir yana cewa: “Na ga manzon Allah (S.A.W) a hajjin bankwana yana kan taguwarsa da shi da Ali (A.S) sai na ji shi ya ce: “Ya ku mutane na bar muku abin da idan kun yi riko da su ba zaku taba bata ba, littafin Allah da Ahlin gidana”[1].

Tirmizi ya ce: A wannan babi kawai an karbo wannan hadisi daga Abi Sa’id da Zaidu dan Arkam da Huzaifa dan Asid.

A sahih Muslim da masnad Ahmad dan Hanbal da sunnan Darimi da Baihaki da wasunsu kuma lafazi ga na farko yake daga Zaid dan Arkam ya ce: “Manzon Allah ya tsaya yana mai huduba a wani ruwa da ake kira Khum da yake tsakanin Makka da Madina…

Sannan ya ce: “Ya ku mutune ku sani ni mutum ne da dan sakon ubangijina ya kusa zuwa sai in amsa masa, na bar muku nauyaya biyu; Na farko littafin Allah da akwai shiriya a cikinsa, ku yi riko da littafin Allah da kuma Ahlin gidana”[2].

A cikin sunan Tirmizi da masnad Ahmad da lafazin Tirmizi: “Na bar muku abin da da idan kuka yi riko da shi ba zaku taba bata ba bayana, daya ya fi daya girma: littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Ahlin gidana, ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske ni a tafki, ku duba ku gani yaya zaku maye mini a cikinsu”[3].

Daga irin hadisai da suka zo akwai hadisin safina. Manzo (S.A.W) yana cewa: “Ku sani misalin Ahlin gidana a cikinku kamar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau ya tsira wanda kuma ya bar shi ya nutse”[4].

Wasu malamai da dama suna ganin Ahlin gidan Annabi (S.A.W) su ne mutum biyar masu girma da daraja da ya hada da annabin kansa (S.A.W) da kuma Ali da sayyida zahara da Hasan da Husain (A.S).

Wannan kuma shi ne mahangar da yawa daga sahabbai, wadanda suka tafi akan hakan sun hada da, Abu Sa’idul khuduri, da Anas dan Malik, da Wasila dan Aska’a, da Ummul muminin Ummu Salama, da A’isha, da Ibn Abi Salama -agolan Annabi- da Sa’ad dan Abi Wakkas, da sauransu.

Ma’abota tafsiri da ruwayar hadisai da dama sun tafi akan hakan daga cikinsu akwai; Faharur razi a littafin Tafsirul kabir, da Zamakhshari a Kusshaf, da Kurdabi a Aljami’u li ahkamil kur’an, da Shaukani a Fatahil kadir, da Tabari a Jam’ul bayan an tawili ayil kur’an, da Suyudi a Durrul mansur, da Ibn Hajar Al’askalani a littafin Isaba, da Hakim a Mustadrak, da Zahabi a cikin Talkhis, da imam Ahmad dan Hanbal a littafin Masnad.

Wannan kuma shi ne ra’ayi da yafi zama daidai, shi ya sa ma zamu gani a ruwayar Muslim a sahihinsa da sanadinsa zuwa ga Amir dan Sa’ad dan Abi Wakkas, daga babansa ya ce: Mu’awiya dan Abi Sufyan ya umarci Sa’ad da ya tsinewa imam Ali (A.S) ya ce: Me ya hana ka ka zagi Aba turab? -Kinaya ce ta imam Ali- Sai Sa’ad ya ce: Amma matukar ina tuna uku da Manzo ya fada game da shi ba zan taba zaginsa ba, wallahi ya zama ina da daya daga cikinsu ya fi mini jajayen dabbobi”.

Na ji Manzo (S.A.W) yana cewa da shi -yayin da ya bar shi a wani yaki- sai Ali ya ce: Ka bar ni tare da mata da yara? Sai Manzo (S.A.W) ya ce da shi: Ba ka yarda ba da cewa matsayinka a wajena kamar matsayin Haruna ne gun musa sai dai babu wani Annabi bayana, Na kuma ji shi (S.A.W) yana fada a ranar haibar: Zan bayar da wannan tuta ga wani mutum da yake son Allah da manzonsa, Allah da manzonsa suke sonsa, ya ce: Sai duk muka yi burinta, sai ya ce: Ku kira mini Ali, sai aka zo da shi yana ciwon ido sai ya yi tofi a idanunsa sannan ya mika masa tutar da Allah ya bayar da nasara a hannunsa, Yayin da ayar Mubahala: “Ka ce ku zo mu kira ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku…” ta sauka sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husain ya ce: Ya Ubangiji wadannan su ne Ahlin gidana”[5].

Tirmizi ya rawaito a sahihinsa da sanadinsa daga Amir dan Sa’ad dan Wakkas ya ce: Yayin da wannan aya ta sauka “Mu kira ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku” sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husain sannan ya ce: Ya Allah wadannan su ne Ahlin gidana”[6].

Haka nan Hakim[7] ya rawaito shi a littafin Mustadrak da Baihaki[8] shi ma a littafin sunna.

Mawallafi littafin Kusshaf yana cewa: Babu wani dalili mafi karfi ga falala da daukaka da ya kai wannan ga ma’abota kisa, Wadanda su ne Ali da Fadima da Hasan da Husain domin su yayin da yayar mubahala[9] ta sauka ya kiransu ya rungume Husain ya rike hannun Hasan, Fadima tana bayansa Ali kuma yana bayanta, da wannan ne aka san ma’anar ayar, kuma ‘ya’yan Fadima da zuriyarsu ana kiransu ‘ya’yansa, kuma ana danganta su ga Manzo dangantawa ingantacciya mai amfani a duniya da lahira[10].

Imam Ahmad ya rawaito a babin falala da sanadinsa daga Shaddad Abi Ammar, ya ce: Na shiga wajan Wasila dan Aska’a, a wajansa akwai wasu mutane sai suka rika maganar Ali (A.S) sai suka zage shi ni ma sai na zage shi tare da su, bayan sun tashi sai ya ce da ni: Ba na ba ka labari ba daga abin da na gani daga manzon Allah (S.A.W) ? Sai na ce: Na’am, Sai ya ce: Na zo wajan Fadima (A.S) ina tambayar ta Ali, sai ta ce ya tafi wajan manzon Allah (S.A.W), sai na zauna na saurare shi har sai da manzon Allah ya zo a tare da shi akwai Ali da Hasan da Husain (A.S), kowannensu yana rike da hannunsa, sai ya zaunar da Hasan da Husain kowanne akan cinyarsa sannan sai ya lulluba masu tufafinsa -ko kuma bargo- sannan ya karanta wannan aya: “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul baiti ya kuma tsarkake ku tsarkakewa”. Sannan sai ya ce: “Ya Ubangiji wadannan su ne Ahlin gidana, Ahlin gidana su suka fi cancanta”[11].

Tabari ya rawaito shi a cikin tafsirinsa[12] da Tirmizi[13] a cikikn sahihinsa, da Suyudi[14] a Durrul mansur, da Haisami a Majma’az zawa’id[15], da Hakim a Mustadrak[16] da Ahmad a Masnad[17].

Amma Abin Da Ya Zo Game Da Nau’i Na Biyu

Hadisin da Manzo (S.A.W) ya fadi adadin imamai a ciki kuma su sha biyu ne

Manzo ya bayar da labarin adadin imamai da zasu zo bayansa da imami kuma halifa bayansa kamar yadda ma’abota sihah (ingantattun littattafai) da ma’abota masanid suka rawaito kamar yadda zai zo:

1-Muslim ya raywaito daga Jabir daga Samura cewa ya ji Annabi (S.A.W) yana cewa: “Addini ba zai gushe ba yana mai tsayuwa har sai alkiyama ta tashi ko kuma an samu halifofi goma sha biyu a gareku dukkaninsu daga kuraish”.

A wata ruwaya sai Annabi ya fadi wata kalma da ban ji ba, sai na tambayi babana: menene manzon Allah ya ce: Sai ya ce: “Dukkaninsu daga Kuraishi suke”[18].

A wata ruwaya ya ce: “Dukkaninsu daga Bani Hashim”[19].

Ahmad da Hakim sun rawaito da lafazin Hakim daga Masruk ya ce: Mun kasance muna zaune a wani dare gun Abdullahi dan Mas’ud yana karanta mana Akur’ani sai wani mutum ya tambaye shi: ya Aba Abdurrahman shin kun tambayi Annabi (S.A.W) halifa nawa ne zai mallaki al’amarin wannan al’umma? Sai Abdullahi ya ce: Tun da na zo Iraki ba wanda ya tambaye ni wannan kafin kai! Sai ya ce: Mun tambaye shi sai ya ce: “Goma sha biyu ne, da adadin zababbun Bani Isra’il”[20].

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com

[1] - Tirmizi: 5\621, Da Kanzul Ummal: 1\48.

[2] - Muslim Babu Fada’ili Ali da Masnad Ahmad: 4\366, Da Sunan Darimi: 2\431, Sunan Baihaki: 2\148, Da 7\30.

[3] - Tirmizi: 5\622, Da Usudul Gaba: 2\12.

[4] - Hakim A Mustadrak: 3\151.

[5] - Sahih Muslim: 15\175-176.

[6] - Sahih Tirmizi: 2\166.

[7] - Mustadrak Hakim: 3\150.

[8] - Sunan Baihaki: 7\63.

[9] - Ali Imran: 61.

[10] - Kusshaf: 1\147-148.

[11] - Imam Ahmad Bn Hanbal: Kitab Fada’ilis Sahaba: 2\557-578.

[12] - Tafsiri Tabari: 22\5-6.

[13] - Tirmizi: 5\351-663.

[14] - Durrul Mansur: 5\198.

[15] - Majma’az Zawa’id: 9\166.

[16] - Mustadrak Na Hakim: 3\147.

[17] - Masnad Ahmad: 4\107.

[18] - Fatahul Bari: 13\181, Da Mustadrak: 3\617.

[19] - Yanabi’ul Mawadda: 3 Babi 77.

[20] - Masnad Ahmad: 1\398, Da 406, Da Fatahul Bari: 16\339.