DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI  JINKAI

TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA MANZON RAHAMA

DA ALAYENSA TSARKAKA

Ahlul Baiti (A.S) a cikin Kur’ani mai girma:

 “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya kuma tsarkake ku tsarkakewa”

Surar Ahzab\ aya: 33

Ahlul Baiti (A.S) a cikin hadisai madaukaka:

 “Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su”

Sahihan Littattafai Da Masanid

Dimuwar Da Suka Samu Game Da Fassarar Hadisin

Malaman makarantar halifofi sun samu dimuwa wajan bayanin abin da ake nufi da goma sha biyu a wannan ruwaya da aka ambata, kuma zantuttukansu suna karo da juna.

Ibnl Arabi ya fada a sharhin sunan Tirmizi: Sai muka kirga bayan Manzo (S.A.W) sai muka samu sarakuna goma sha biyu sai muka samu Abubakar, Umar, Usman, Ali, Hasan, Mu’awiya, Yazid, Mu’awiya dan Yazid, Marwan dan Hakam, Abdulmalik dan Marwan, Walid, Sulaiman, Umar dan Abdul-Aziz, Yazid dan Abdulmalik, Marwan dan Muhammad dan Marwan, Assaffah…

Anan sai ya kirga halifan ishirin da bakwai na Abbasawa zuwa zamaninsa sannan sai ya ce: Idan muka kiraga goma sha biyu, adadin ya kare daga Sulaiman amma idan muka kirga su da daukaka to akwai biyar daga halifofi wato halifofi hudu da Umar dan Abdul-Aziz amma ni kam ban gane wani abu ba game da wannan hadisi[1].

Alkali Iyad yana fada game da amsar wani wanda ya ce: adadin da suka yi mulki sun wuce hakan. Da cewa; wannan magana ba ta da hujja, domin Manzo bai ce goma sha biyu ne kadai zasu yi mulki ba, don haka ba abin da zai hana su fi hakan yawa[2].

Shi ma Suyudi yana bayar da amsa game da hakan ya ce: Abin da ake nufi da sha biyu ana nufin halifofi sha biyu a dukkan zamanin musulunci har zuwa ranar alkiyama da zasu yi aiki da gaskiya koda kuwa ba a jere suke ba[3].

A littafin Fathul Bari: Halifofi hudu sun gabata kuma ba makawa da cikon saura kafin alkiyawm ta tashi[4]. Ibnul Jauzi ya ce: Akan haka abin nufi da sannan sai bala’i ya faru ita ce fitina da zata faru kafin alkiyama na daga bayyanar Dujal da abin da zai biyo baya[5].

Suyudi ya ce: Daga sha biyu an samu halifofi hudu da Hasan da Mu’awiya da Ibn Zubair da Umar dan Abdul-Aziz wadannan takwas kenan, sannan akwai tsammanin Mahadi na Abbasiyya, domin shi a cikin Abbasawa kamar Umar dan Abdul-Aziz ne a Bani Umayya, saboda adalcin da yake da shi, sai ya zama biyu ne suka rage wanda yake daya daga cikinsu Mahadi ne saboda shi yana daga cikin Ahlul Baiti (A.S)[6]. An ce: Abin da ake nufi da halifa goma sha biyu a muddar izzar musulunci da karfinsa da kuma daidaituwar al’amura da ya hada da duka wanda musulunci ya samu izza a zamaninsa, musulmi suka hadu akan halifancinsa[7].

Baihaki ya ce: An samu wannan adadi da wannan siffa da aka ambata har zuwa lokacin Walid dan Yazid dan Abdulmalik, sannan sai aka sami fitina mai girma, sannan sai mulkin Abbasawa ya bayyana, kuma su suna da yawa da sun wuce wannan adadi da aka fada[8].

Suka ce: Wadanda aka yi ittifaki a kansu na daga halifofi uku ne sannan sai Ali har lokacin da aka samu al’amarin hakamaini a yakin Siffaini sannan sai Mu’awiya ya yi da’awar mulki.

Sannan sai suka yi ittifaki akan Mu’awiya yayin sulhunsa da Hasan (A.S), sannan sai dansa Yazid, amma Husain (A.S) bai samu mulki ba saboda an kashe shi, sannan sai bayan mutuwar Yazid suka yi sabani har sai da suka hadu akan Abdulmalik dan Marwan bayan kashe dan Zubair, sannan sai suka yi ittifaki akan ‘ya’yansa hudu; Walid, sannan sai Sulaiman, sannan sai Yazid, sannan sai Hisham, sai Umar dan Abdul-Aziz da ya shiga tsakanin Sulaiman da Yazid, na goma sha biyu shi ne Walid dan Yazid dan Abudulmalik da mutane suka yi ittifaki akan jagorancinsa bayan Hisham da ya yi mulki shekara hudu[9].

Saboda haka halifancin goma sha biyu ya zama ingantacce da ittifakin musulmi akan su, kuma Manzo ya yi albishir ga msulumi da halifancinsu akan riko da musulunci zuwa ga mutane.

Ibn Hajar ya ce: Wannan ra’ayi yana daga mafi kyawon ra’ayi.

Ibn Kasir ya ce: Abin da Baihaki ya tafi akai kuma wasu jama’a suka goya masa baya na cewa abin da ake nufi da halifofi goma sha biyu da aka ambata a wannan hadisi su ne masu jerantuwa har zuwa Walid dan Yazid dan Abdulmalik fasiki da magana ta gabata akansa da ya shahara da fasikanci da miyagun halaye abu ne wanda yake akwai kokwanto a kansa, domin halifofi har zuwa lokacin Walid dan Yazid sun fi haka yawa kuma dalilin da ya kawo cewa halifofi hudu na farko ne sannan sai Hasan bayansu, domin Ali ya yi wasiyya da shi, sannan sai mutanen Iraki suka yi masa bai’a har zuwa sulhunsu da Yazid dan Mu’awiya, sannan sai Mu’awiya dan Yazid, sannan Marwan dan Hakam sannan dansa Abdulmalik dan Marwan, sai dansa Walid dan Abdulmalik, sai Sulaiman dan Abdulmalik, sannan sai Umar dan Abdul-Aziz, sannan sai Yazid dan Abdulmalik, sannan sai Hisham dan Abdulmalik, wadannan sha biyar kenan, sannan Walid dan Yazid dan Abdulmalik, sannan idan muka yi la’akari da dan Zubair kafin Abdulmalik sun zama goma sha shida, ta kowane hali su goma sha biyu ne kafin Umar dan Abdul-Aziz, wanda Yazid dan Mu’awiya ya shiga cikin sha biyu, kuma Umar dan Abdul-Aziz ya fita daga cikinsu, wanda al’umma suka yi ittifaki a kan gode masa da yabonsa suka kuma kirga shi cikin halifofi shiryayyu, kuma al’umma ta hadu akan adalcinsa, kuma lokacin yana daga mafi adalcin zamuna hatta da rawafidawa suna furuci da hakan. Idan Baihaki ya ce: Mu ba ma la’akari da wanda al’umma ta yi ittifaki a kansa, to dole ne ya cire Ali da dansa Hasan daga cikinsu domin su ma al’umma ba ta yi ittifaki a kansu ba, domin mutanen Sham gaba dayansu ba su yi musu bai’a ba.

Ya ce: Wasu kuma sun sanya mu’awiya da dansa Yazid da dan dan’uwansa Mu’awiya dan Yazid, ba tare da sun kayyade lokacin Marwan ba ko kuma dan Zubair, domin al’umma ba ta yi ittifaki akan daya daga cikinsu ba, saboda haka muna iya cewa wannan kirga na halifofi uku, sannan sai Mu’awiya, sai Yazid, sai Abdulmalik, sai Walid dan Sulaiman sai Umar dan Abdul-Aziz, sai Yazid, sai Hisham wadannan goma kenan, sannan bayansu akwai Walid dan Yazid fasiki, sai ya zama dole ne ga malam Baihaki ya fitar da Ali da dansa Hasan daga ciki wadannan kuma ya saba wa abin da malaman sunna da na shi’a suka tafi a kai[10].

Ibnul Jauzi ya fitar a littafin Kashful mushkil ta fuska biyu:

Na daya: Cewa Manzo (S.A.W) yana nuni da wadannan hadisai zuwa ga abin da zai faru bayansa da bayan sahabbansa, kuma hukunci da aka fada a wannan labari yana nuni zuwa ga abin da zai faru ne bayansu ne, kamar yaddda ya yi nuni da adadin halifofin Bani Umayya, kuma kamar fadinsa na cewa: “Addini ba zai gushe ba…”. Ai shugabanci da halifofi goma sha biyu zasu yi sannan sai ya koma zuwa ga halin da ya fi wannan muni, kuma farkon Bani Umayya shi ne Yazid dan Mu’awiya zuwa Marwanal himar, kuma adadinsu su goma sha uku ne, ba kuma za a sa Usman ko Mu’awiya ko dan Zubair a cikinsu ba saboda su sahabbai ne, idan muka fitar da Marwan dan Hakam daga cikinsu saboda sabanin da aka samu akan halifancinsa, ko kuma domin shi an rinjaye shi bayan mutane sun yi ittifaki a kan Abdullahi dan Zubair to adadi ya inganta, yayin da aka fitar da mulki daga Bani Umayya sai fitina mai girma ta faru yakoki suka yawaita har sai da daular Bani Abbas ta tabbata hali ya canja daga yanda yake canji bayyananne.

Ibn Hajar ya yi raddi akan wannan dalili[11] a littafin Fatahul bari.

Na biyu: Ibn Jauzi ya nakalto a juzu’in da Abul-Husaini dan Al-munadi ya tattaro a littafin Al-mahadi, yana cewa: Akwai tsammanin cewa wannan zai faru ne bayan Mahadi da zai bayyana karshen zamani, ya ce: Na samu a cikin littafin Daniyal: Idan Mahadi ya mutu bayansa mutane biyar daga ‘ya’yan babban jika zasu yi mulki, sannan sai biyar daga ‘ya’yan jika karami, sannan sai ya yi wasiyya da halifanci ga wani mutum daga ‘ya’yan jika babba, sannan sai dansa ya yi mulki bayansa, sai ya zama an sami mulki goma sha biyu kowanne imami ne mai shiryarwa.

Ya ce: A wata ruwaya sai mutum sha biyu su yi mulki, shida daga ‘ya’yan Hasan, biyar daga ‘ya’yan Husain wani kuma daga waninsu, sannan sai ya mutu sai zamani ya lalace.

Ibn Hajar ya yi ta’aliki akan wannan hadisi ya ce: Wannan ruwaya tana da rauni kwarai ba za a iya dogara da ita ba[12].

Wasu mutane suka ce: Zai iya yiwuwa Manzo (S.A.W) yana bayar da labarin abubuwan mamaki da zasu faru da fitinu har mutane a lokaci guda su rarrabu da sarakuna goma sha biyu, da yana nufin wanin hakan da ya ce goma sha biyu da zasu yi kaza da kaza, saboda haka ba komai yake nufi ba sai su zama a lokaci daya…”[13].

Suka ce: Ya taba faruwa a karni na biyar a Andulus kadai akwai sarakuna shida kowanne yana cewa shi ne sarki, akwai kuma na Misira da na Abbasiyya a Bagdad banda wanda yake da’awar shugabanci a duniyar musulmi na daga Alwiyyawa da Hawarijawa[14].

Ibn Hajar ya ce: “Wannan zance ne na wanda bai san wata hanya da wannan hadisi ya zo ba in banda ruwayar da ta zo daga cikin littafin Sahihul Buhari kawai”[15].

Samuwarsu a lokaci guda tana samar da rarraba ne ba zai yiwu ya zama shi ne abin da ake nufi ba[16]. Haka nan ba su yi ittifaki ba akan wani ra’ayi da ya zo na daga bayanan da suka gabata, sai dai sun yi kokarin rufe ido da kawar da kai daga ruwayar da ta zo daga Annabi (S.A.W) da sunayensu domin ta saba da siyasar Hukuma da Dauloli a Koyarwar halifanci a tsayin zamani, Malaman hadisai sun fitar da wannan ruwayoyi a littattafansu da sanadinsu zuwa ga manyan sahabbai daga manzon Allah (S.A.W)[17].

Abin Da Ya Zo Game Da Nau’i Na Uku

Daga Abi Abdullahi Assadik (A.S) ya ce: Jibril ya sauka wajan Muhammad (S.A.W) sai ya ce: Ya Muhammad! Allah yana yi maka albishir da abin haihuwa da za a haifa daga Fadima (A.S) wanda al’ummarka zata kashe shi bayanka, sai ya ce: Ya Jibril! Aminci ya tabbata ga Ubangiji na ba bukata gareni ga abin haihuwa da al’umma ta zata kashe shi bayana, sai ya Jibril ya hau ya sauka, sannan sai ya sake fada masa hakan. Sai ya ce: Ya Jibril! Aminci ya tabbta ga ubangijina ba ni da bukata ga irin wannan abin haihuwa da al’ummata zata kashe shi. Sai Jibrilu ya hau ya sake sauka ya ce: Ya Muhammad Ubangijinka yana gaishe da kai yana kuma yi maka albishir da cewa zai sanya imamanci da shugabanci da wasiyya a cikin zuriyarsa, sai ya ce: Na yarda. Sannan sai ya aikawa Fadima (A.S) cewa Allah yana yi mini albishir da da da za a haifa daga gareki, da al’ummata zata kashe shi bayana, sai ta aika masa da cewa babu bukata gareni ga wannan da da al’ummarka zata kashe shi bayanka, sai ya aika mata da cewa, Allah ya sanya imamanci da shugabanci da wasiyya a cikin zuriyarsa, sai ta aika zuwa gareshi da cewa na yarda “Babarsa ta dauki cikinsa tilas ta haife shi tilas kuma cikinsa da yaye shi wata talatin ne har sai da ya isa karfinsa ya kai shekara arba’in sai ya ce: ka sanya mini in gode wa ni’imarka da ka yi mini da ni da iyayena, kuma in aikata aiki na gari da zaka yarda da shi, kuma ka gyara mini a cikin zuriyata”[18]. Ba domin ya ce ka gyara mini a cikin zuriyata ba, da dukkan zuriyarsa sun zama imamai[19].

Shi’a suna imani da cewa kowane imamai ya yi wasiyya da imamin da zai zo bayansa[20].


Sunayen Imamai Goma Sha biyu Daga

Ruwayar Ahlussuna

1- Jawini[21] ya rawaito daga Abdullahi dan Abbas ya ce: manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ni ne shugaban annabawa Ali dan Abi talib shugaban wasiyyai, kuma wasiyyaina goma sha biyu ne bayana na farkonsu shi ne Ali dan Abi Talib na karshensu Mahadi”.

2-daga dan Abbas ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Halifofina kuma wasiyyaina kuma hujjojin Allah bayana goma sha biyu ne na farkonsu dan’uwana na karshensu dana”. Sai aka ce ya manzon Allah wanene dan’uwanka? Sai ya ce: Ali dan Abi Talib, Aka ce wanene danka? Ya ce: Mahadi wanda zai cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci, na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya mai albishir da gargadi, da ya kasance bai rage ba daga duniya sai rana daya da Allah ya tsawaita ranar har sai dana Mahadi ya bayyana sai Ruhul-Lahi Isa dan Maryam ya sauka, sai ya yi salla bayansa kuma kasa zata haskaka da hasken Ubangijinta kuma ikonsa zai kai gabas da yamma”.

3- Jawini da sanadinsa ya ce: Na ji manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Ni da Ali da Hasan da Husain da tara daga ‘ya’yan Husain tsarkaka ne ma’asumai”[22].

Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice

Allah bai halicci mutum domin wasa ba, kadai ya halicci mutum domin ibada ne da shiriya. Annabta tana dauke da nauyi ne na gargadi da isar da sakon Allah, imamanci kuma yana dauke da shiryar da mutane zuwa ga wannan shiriya da kuma kama hannun mutane domin su bi wannan shiriya da annabawa suka zo da ita a aikace. Ba zai yiwu a san annabta ba sai da wahayi da mu’ujiza, kuma ba zai yiwu a san imamanci ba sai da nassi da yake nuna ma’sumi.

Bai’a ga shugaba ma’abocin wilaya ta gaskiya ba wai ita ke tabbatar da wajabcin binsa ba[23] a matsayinsa na imami da Annabi ya yi wasiyya da shi da binsa, kamar yadda ba ta iya tabbatar da imamanci da halifancinsa ba[24]. Amma shura ba ta iya zama maimakon wasiyya kamar yadda hukuncin da shura take zartarwa ba ya zama wajibi ga imami ya bi.

Manzo (S.A.W) ya yi aiki domin karfafa nassi da wasiyya a kwakwalen musulmi ne, sannan tarihi bai taba tabbatar da zuwan wani abu daga gareshi ba game da wasiyya sai dai nassi da hadisi.

Amma imam Ali aikinsa gaba daya ya tsayu akan nazarin nassi da hadisi ne yayin da zamu ga yana musun duk wani abu da ya sabawa hakan.

Daga karshe mun samu dalili na ruwayoyi daga shi’a da sunna da suke tabbatar da halifanci da imamanci ga imamai goma sha biyu da nassin hadisin Annabi (S.A.W) wanda na farkonsu yake Ali dan Abi talib na karshensu Mahadi (A.S) da wannan ne wannan nazari da mahanga zata zama ita kadaice hanyar shari’a da take tabbatar da hanyar ibada da shiriya.

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com

[1] - Sharh Bn Arabi Ala Sunan Tirmizi: 9\68-69.

[2] - Sharh Nawawi Ala Muslim: 12\201-202.

[3] - Tarihul Khulafa Na Suyudi: 12.

[4] - Tarihul Khulafa Na Suyudi: 12.

[5] - Tarihul Khulafa Na Suyudi: 12.

[6] - Assawa’ikul Muhrika: 19, Da Tarihul Hulafa Na Suyudi: 12.

[7] - Sharhi Muslim: 12\202-203, Da Suyudi A Tarihul Hulafa: 10.

[8] - Tarihu Ibn Kasir: 6\249, Daga Baihaki.

[9] - Tarihul Hulafa: 11, Da Sawa’ikul Muhrika: 19, Da Fatahul Bari: 16\341.

[10] - Tarihu Ibn Kasir: 6\249-250.

[11] - Fatahul Bari: 13\183.

[12] - Fatahul Bari: 13\184, Da Sawa’ikul Muhrika: 19.

[13] - Fatahul Bari: 16\338.

[14] - Sharhin Nawawi: 12\202, Fatahul Bari: 16\339.

[15] - Fatahul Bari: 13\182.

[16] - Fatahul Bari: 13\182.

[17] - Ma’alimul Madarasatain: 1\541-546.

[18] - Ahkaf: 15.

[19] - Usulul Kafi: 1\465.

[20] - Usulul Kafi: 1\286.

[21] - Tazkiratul Huffaz: 5\150.

[22] - Hadisai: 1, 2, 3, Da Suka Zo A Fara’idussimdaini: 2\312.

[23] - Shi kamar ka’aba ce, tana nan a ka’abar ta mutane sun zo sun yi dawafi a gefenta ko ba su yi ba. Hafiz Muhammad.

[24] - Imami yana nan imami da Allah shi ne ya yarda da shi, ko mutane sun yi masa bai’a sun bi shi ko ba su yi ba, kamar yadda yake game da annabawa ko an bi su an yi musu bai’a ko ba a yi musu ba, wannan ba ya nuna cewa ba su ne suka cancanci bi ba ko su ne.