DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI� JINKAI

TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA MANZON RAHAMA

DA ALAYENSA TSARKAKA

Ahlul Baiti (A.S) a cikin Kur�ani mai girma:

��Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya kuma tsarkake ku tsarkakewa�

Surar Ahzab\ aya: 33

Ahlul Baiti (A.S) a cikin hadisai madaukaka:

��Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su�

Sahihan Littattafai Da Masanid

Nazarin Nassi Da Wasiyya A Hadisan Imam Ali (A.S) Da Ahlul Baiti (A.S)

�Abu ne a fili ga wanda ya karanta tarihi cewa imam Ali shi ne wanda ya bayyanar da hadisai da suke nuna halifancinsa bayan Manzo da sunansa (A.S) kuma ingancin wannan wani abu ne da ma�abota ilimi na wannan al�umma da suka fitar da son rai daga zukatansu suka tabbatar da shi, kuma sama da malami hamsin daga masu sharhin hadisansa sun yi bayanin haka suka kuma kare wannan kariya mai cike da hujjoji da dalilai da suka bayar da nutsuwa akan hakan[1].

Ali (A.S) shi ne wanda ya dawo wa kwakwalen mutane batun hadisan halifancinsa ba tare da wata jayayya ba, bayan an hana fadin wadannan hadisai a lokacin halifofi da suka gabace shi, yayin da suka hana fadin hadisan manzon Allah sai wanda ya shafi ibada kadai:

1- Ya tara sahabban manzon Allah lokacin halifancinsa sannan ya yi musu huduba yana mai hada su da Allah cewa waye ya ji Manzo (S.A.W) a Gadir khum yana cewa; �Duk wanda nake shugabansa Ali shugabansa ne�, sai ya tashi ya shaida[2].

2- Ali shi ne ya yada wannan hadisin da ya bujuro da shi ga Abubakar da Umar da Annabi yake cewa akwai wanda a cikinku zai yi yaki akan tawilin Kur�ani kamar yadda na yi yaki akan saukarsa wanda Abubakar ya yi burin a ce shi ne, haka ma Umar, amma Manzo ya amsa musu da: A�a. Sannan daga baya Manzo ya gaya wa mutane cewa Ali (A.S) ne[3].

Wannan ruwaya duk da waninsa sun rawaito ta amma ruwayarsa tana da wani hususiyya domin ya yi ta ne a huduba a gaban mutane, ba hadisi ba ne da ya gaya wa mutum daya ko wasu jama�a, wannan kuwa yana karfafa karfin hadisi game da hakkinsa da yake da yakini da shi, kuma yake da yakini da cewa sauran sahabbai suna da yakini da hakan ba su manta ba.

3- Kuma ya ambaci dayawa daga wadannan hadisai da suke nuna hakkinsa a ranar shura ko bayanta, sai dai an yi sabani kan dalla-dallar maganar da isnadinsa, duk da a dunkule sun tabbatar da hakkinsa, mafi karancin abin da ya hada su da Allah akansa shi ne abin da Ibn Abdulbar ya fitar a littafinsa yana mai cewa: Ali ya fada wa wadanda suke cikin shura tare: �Ina hada ku da Allah shin akwai wanda Manzo (S.A.W) ya hada shi �yan�uwantaka da shi tsakaninsa da shi yayin da ya sanya �yan�uwantaka tsakanin musulmi in ba ni ba?

A bayan wannan hadisi Ibn Abdulbar ya sake rawaito wani daga Ali yana mai cewa: Imam Ali (A.S) ya kasance yana cewa: �Ni bawan Allah ne kuma dan�uwan manzonsa, ba mai fadin haka a bayana sai makaryaci�[4].

An rawaito ta a littafin Kanzul Ummal a wani hadisi mai tsayi daga abittufail ya ce ali (A.S) ranar shura yana fadin wannan hadisi�[5].

Wanda abin da shi Ibn Abdilbar ya fitar wani yanki ne daga gareshi, sai dai sanadin Kaznul ummal a kwai jahala[6] a cikinsa, shi ya sa ma aka samu jayayya game dashi, ance Zafir ya rawaito shi wanda shi mutum ne da ba a san shi ba, wasu kuma sun yi musunsa saboda mataninsa amma ba a la�akari da wannan saboda ya ginu ne akan fahimta ta cewa an yi bai�a ga Abubakar akan cewa ijma�i ce ko kusa da hakan wacce ba ta da asasi.

Amma isnadi ya kasance saboda Zafir ne kamar yadda Ibn Abdilbar ya rawaito shi a littafin Isti�ab,[7] Ibn Hajar Askalani ya ce: Zafir ba a tuhumar sa da karya, kuma idan aka same shi a hadisi to hadisinsa yana da kyau[8].

A farkon wannan hadisin, Abu Tufail yana cewa: Na kasance a bakin kofa ranar shura sai aka daga sauti sama, sai na ji Ali (A.S) yana cewa: �Mutane sun yi bai�a ga Abubakar amma na rantse da Allah ni na fi shi cancanta, amma sai na ji na bi domin tsoron kada su koma kafirai wasu suna saran wasu da takobi, sannan sai Umar ya biyo bayansa alhalin na fi shi cancanta kan wannan al�amri, amma sai na ji na bi tsoron kada mutane su koma kafirai wasu suna saran wasu, sannan sai ga ku kuna son ku yi bai�a ga Usman! Ba komai zan ji in bi�, Sannan sai ya ambaci al�amrin shura ya fara bayyana musu falalarsa da fifikonsa da darajojinsa da ya fi su da ita, daya daga cikinsu ita ce wannan bangaren da shi Ibn Abdilbar ya rawaito game da �yan�uwantakarsa da Manzo (S.A.W)[9]. Wannan hadisi yana da wani mai karfafarsa da zai zo nan gaba.

4- Daga abin da yake nuna cancantarsa fiye da Abubakar musamman yayin da ya fadi karbar surar bara�a daga Abubakar!

Nisa�i ya rawaito da sanadi sahihi daga Ali (A.S) cewa manzon Allah (S.A.W) ya aika shi da bara�a zuwa ga mutanen Makka tare da Abubakar, sannan sai ya sa Ali ya bi shi ya ce da shi: �Ka karbi littafin ka tafi zuwa Makka ya ce: Sai ya cim masa a hanya, sai Abubakar ya koma Madina yana mai bakin ciki, sai ya ce: An saukar da wani abu game da ni ne? Sai Manzo ya ce: A�a, sai dai ni an umarce ni da in isar da wannan ko ni ko wani mutum daga gidana�[10].

A dukkan wannan hadisai akwai raddi ga wanda ya ke cwa Ali bai ambaci wani abu ba da yake nuna shi ya fi cancanta da halifanci, wannan kenan balle mu shiga Nahajul Balaga.

5- Daga mafi shaharar maganarsa bayan labarin Sakifa ya zo masa da kuma mubaya�ar da mutane suka yi wa Abubakar:

ya ce: Me kuraishawa suka ce?

Suka ce: Sun kafa hujja da cewa su ne bishiyar Manzo.

Sai ya ce; Sun kafa hujja da bishiya amma sun tozarta �ya�yan itaciyar[11].

6- Kafa hujja da sakamakon Sakifa a fadinsa:

□Idan ka shugabance su sakamakon shura

□Yaya haka alhalin masu shawara ba sa nan

□Idan kuma ka kafa hujja garesu da kusanci ne

□To waninka shi ne ya fi cancanta da kusanci[12].

7- Hudubar shakshakiyya wacce take da karfafuwa daga malamai[13] daban-daban kuma take da ma�ana da take nuni ga hakan a fili dalla-dalla:

�Amma wallahi! Hakika wane ya sanya ta �rigar halifanci-{kamar yadda ake sanya riga} alhalin kuma ya san cewa misalin matsayina game da ita kamar matsayin kan inji ne na nika da dutsensa, kwararar ambaliyar ruwa daga gare ni yake gangarowa kuma tsuntsu ba ya iya kaiwa wajena {duk tashinsa}, amma sai na sakaya tufafi na kau da kai[14] na kuma cije na kawar da kai, na zama ina mai kai-kawon ko in tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu�!

Sai na ga hakuri akan wannan ya fi lizimtuwa, sai na yi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kuma shakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa! har sai da na farko ya wuce, sai ya mika ta zuwa ga wane bayansa�

Abin mamaki! Yayin da ya kasance yana neman ya sance ta daga wuyansa[15] a rayuwarsa sai ga shi ya kulla (mika) ta ga wani bayan wafatinsa, ya mamakin tsananin yadda suka yi kashe mu raba na abin da yake cikin hantsarta�![16]

Sai na yi hakuri tsayin lokaci, da tsananin jarabawa, har sai da ya wuce shi ma sai ya sanya al�amarin halifanci a hannun wasu jama�a da ya raya cewa (wai) ni daya ne daga cikinsu, Kaicon al�amarin shura!, yaushe ne kokwanton fifikon al�amarina akan na farkonsu ya faru har da zan zama ana sanya ni tsaran makamantan wadannan!��[17].

Ashe kenan Abubakar ya san matsayin imam Ali na halifanci da daukakarsa kamar yadda kan dutsen markade da nika yake da daukaka akan jikin dutsen ne.

Saoba haka ne yake a fili cewa matsayinsa ba boyayye ba ne sai dai mun ga tarihi yan neman ya farar da wani abu na jayayya domin ya yi daidai da abin da ya faru a tarihi, kamar yadda muka samu wasu suna neman musun maganarsa a game da halifanci, wanda da can sun yi musu ga hadisan Manzo (S.A.W). Amma gaskiya tana nan, sai dai abin takaici da tarihi bai karkata zuwa ga Ali ba! Tarihin da ya riga ya tabbatar da cewa imam Ali bai yi bai�a ga Abubakar sai bayan wata shida, sai ya nemi toshe kunnensa game da wannan jinkiri da imam Ali ya yi!

8- Maganarsa bayan shura, yayin da suka yi wa Usman bai�a yana mai cewa: �Wallahi kun sani ni na fi cancanta fiye da wanina, wallahi zan yi hakuri matukar al�amarin musulmi ya kubuta zalunci ya kasance a kaina ne ni kadai, domin neman ladan Allah da falalarsa, da kuma nisantar abin da ya ke kuna goggoriyonsa na kawa da adonsa�[18].

Ibn Abil Hadid ya samu wannan kalma cikin karshen abin da Ali ya fada a wannan lokaci a maganar da ya nakalto ta a nan bayan ya kawar da duk wani kokwanto game da ingancinta, sai ya ce: Mu muna ambaton wannan abu da ya zo na ruwayoyi masu yawa na imam Ali da ya hada ma�abota shura da Allah, kuma mutane da dama sun rawaito wannan da yawa, amma abin da ya inganta bai kasance da tsayi ba kamar yadda aka rawaito, sai dai bayan sun yi bai�a ga Usman shi ya ki bai�a ya ce: �Mu muna da hakki da in an ba mu sai mu karba, amma idan aka hana mu shi sai mu hau bayan rakuma komai nisan tafiya�.

Sannan sai ya ce da su: �Ina hada ku da Allah shin a cikinku akwai wanda Manzo ya sanya shi dan�uwa tsakaninsa da shi in ba ni ba?

Suka ce: A�a.

Ya ce: A cikinku akwai wanda Manzo ya ce: Duk wanda nake shugabansa wannan shugabansa ne in ba ni ba?

Suka ce: A�a.

Ya ce: Acikinku akwai wanda Manzo (S.A.W) ya ce: Kai a wajena kamar matsayin Haruna ne gun musa, in ba ni ba?

Suka ce: A�a.

Ya ce: Shin a cikinku akwai wanda aka amincewa ya isar da surar bara�a kuma Manzo ya ce: Kuma ba wanda zai isar daga gare ni sai ni ko wani mutum daga gareni, in ba ni ba?

Suka ce: A�a.

Ya ce: Shin ba ku sani ba cewa sahabban Manzo sun gudu sun bar shi a filin daga[19] ba wanda ya rage tare da shi in ba ni ba, ban taba guduwa ba?

Suka ce: E.

Ya ce: Shin kun sani cewa ni ne farkon musulunta?

Suka ce: E.

Sai ya ce: Waye ya fi kusanci da Manzo?

Suka ce: Kai ne.

Sai Abdurrahman dan Auf ya katse maganarsa ya ce: Ya Ali! mutane ne suka zabi Usman, kada ka dora wa �damu- kanka laifi.

Sannan sai Abdurrahman ya kalli Abu Dalha Al�ansari[20] ya ce da shi: Ya Aba Dalha da menene Umar ya umarce ka?

Sai ya ce: In kashe duk wanda ya saba wa al�umma!

Sai Abdurrahaman dan Auf ya ce da imam Ali: Ka yi bai�a tun da haka ne, in ba haka ba sai ka zama wanda bai bi tafarkin musulmi ba! Kuma mu zartar da umarnin da aka umarce mu da shi a kanka!!

Sai Ali (A.S) ya ce: �Kun sani ni ne mai wannan hakki ba wani ba, wallahi zan yi hakuri matukar al�amarin musulmi ya tafi daidai zalunci ya zamanto a kaina ne kawai��[21].

Wannan kuma hadisi jama�a da yawa suka rawaito shi, ba ya cikin raunanansu ko wadanda ake kokwanto.

9- Wani ya taba cewa da imam Ali ya dan Abi talib kai ka kasance mai kwadayin wanna shugabanci, sai ya ce: Ku ne kuka fi ni kwadayinsa kuma ku ne mafi nisa, amma ni na fi kusanci, kuma ina neman hakkina ne, ku kuma kuna hana ni, kuna juyar da fuskata daga gareshi, yayin da ya kafa masa hujja a cikin mutane sai ya juya yana dimuwa bai san me zai amsa ba�[22].

Ahlussunna sun ce wanda ya fadi haka shi ne Sa�ad dan Abi Wakkas ranar shura, Shi�a kuma sun tafi a kan Abu ubaida ne bayan Sakifa, kowanne ne gaskiya dai muhimmin abu ne wanda ya shahara da kowa sunna da shi�a suke rawaito wa kamar yadda Ibn Abil Hadid wanda ya ke sunna kuma bamu�utazili yake rawaitowa[23].

10- Fadinsa: �Ya Ubangiji! ni ina hada ka da kuraishawa da wanda ya taimaka musu, sun yanke zumuncina sun karanta matsayina, sun hadu akan kwace mini abin da yake nawa ne, sannan suka ce: Ka karba da gaskiya ko ka bari da gaskiya[24],

11- Fadinsa: �Amma bayan haka� Yayin da Allah ya karbi ran annabinsa (S.A.W) sai muka ce mu ne ahlinsa masu gadonsa zuriyarsa majibita al�amarinsa ba wani ba, ba mai yi mana jayayya kan shugancin Muhammad, kuma kada wani ya yi kwadayin hakkinmu, sai mutanenmu suka mike suka kwace mana hakkinmu na shugabanci, sai ga shugabancin a hannun waninmu��.

Wannan duk yana daga hudubobin da imam Ali ya yi a Madina a farkon shugabancinsa a lokacin bai fi watanni da karbar halifanci ba[25].

12- Fadinsa: �Amma kwace mana wannan matsayi� wannan wani abu ne da kwadayin mutane ya jawo shi, wasu kuma suka yi bakin ciki kan matsayinmu, alhali hukunci na Allah ne, kuma makoma a alkiyama tana nan gareshi�. Ya fadi wanna a jawabin wanda ya tambaye shi: Yaya mutane suka ture ku gabarin wannan matsayi alhali ku kuka fi cancanta da shi.

Sannan sai imam Ali ya cigaba da magana kan wani abin da ya fi ban mamaki na wannan zamani da kamar Mu�awiya zai zo yan jayayya da shi, yana mai cewa �Zamani ya kai munzalin da yanzu ya ba shi dariya bayan ya sa shi kuka��[26].

Game Da Ahlul Baiti (A.S)

Kamar yadda ya bayyana a fili na karfafa wa ga hakkinsa musamman, matsayin Ahlul Baiti (A.S) yana iya bayyana ga remu daga wadannan kalmomi da suka zo daga gareshi:

1- Fadinsa: �Haka yake, duniya ba za ta taba zama ba hujjar Allah ba a cikinta, ko zahiri mash�huri ko kuma boyayye, domin kada hujjar Allah da ayoyinsa su bace�[27]. Ibn Abil Hadid malamin sunna ne amma yana cewa a nan kusan imam Ali (A.S) ya yi nuni da bin mazhabar shi�a isna ashariyya ne[28].

2- Fadinsa: �Ba a kwatanta alayen muhammad da wani daga wannan al�umma su ne asasin addini kuma madogarar yakini� Su ke da hakkin wilaya da jagoranci, kuma wasiyya da gado na su ne��[29].

Bayan ambaton hakkin jagoranci, wanan al�amari wani abu ne da imam Ali ya yi bayaninsa a fili ko ya yi nuni[30] da shi, amma sai ga shi irin su Dakta Ammara yana neman ya gafala daga wannan hudubobi na imam Ali (A.S) yana neman nuna rashin samun magana ta karara akan hakan, Da kuma neman kare kagen da ya yi domin ya nuna kalmar �wasiyyi� da ta zo a hadisiddar, da cewa kage ne na shi�a da suka sanya kalmar wasiyyi maimakon waziri[31] alhalin hadisin da ya zo daga ruwayar Ahlussunna bai zo da wata kalma ba in banda kalmar wasiyyina[32].

3- Hadisin �shugabanni daga kuraishawa ne, kuma suna cikin Bani Hashim, ba na waninsu ba ne, kuma shugabanci ba ya yiwuwa ga waninsu�[33]. Mun riga a baya mun yi nuni da wasu hadisai da suka nuna duk wani fifiko da cancantar Bani Hashim akan sauran kuraishawa.

4- Fadinsa (A.S): �Ina zaku ne! Yaya kuke kirar karya! Ga hujjoji a fili, ga ayoyi karara, ga manarori a kafe, yaya ake dimuwa da ku?! Yaya kuka makance alhali a cikinku akwai zuriyar annabinku, su ne jagororin gaskiya, kuma alamomin addini, harsunan gaskiya?! Ku sanya su a matsayi mafi kyau na Kur�ani, ku kuma gangaro zuwa garesu irin gangarowar nan ta mai kishirwa. Ya ku mutane ku rike ta daga cikon annabawa (S.A.W): cewa duk wanda ya mutu daga cikinmu ba matacce ba ne, kuma duk wanda ya rididdige a cikinmu ba rididdigagge ba ne�[34].

A cikin wannan akwai abin takaici da imam (A.S) ya yi nuni da shi ga wadanda suka bar Alayen Annabi (A.S) bayan hujja da dalilai masu karfi bayyanannu da suke wajabta bin su.

5- Fadinsa: �Mu kama ce ta tsatson ma�abota jirgin ruwa, kamar yadda wanda ya ke cikin can ya tsira haka ma wanda ya ke cikin wannan zai tsira, azaba ta tabbta ga wanda ya bar mu� kuma ni a cikinku kamar kogo ne na Ashabul kahafi, kuma ni kamar kofar hidda ce, da wanda ya shige ta ya tsira wanda ya ki ya halaka, ni hujja ce daga watan zilhija a hajjin bankwana da fadin Annabi (S.A.W) cewa: �Ni na bar muku abin da idan kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba a bayana har abada; littafin Allah da kuma Ahlin gidana�[35].

6- Hudubarsa (A.S): �Ku duba Ahlin gidan Annabinku, ku lizimti tafarkinsu, ku bi sunnarsu, ba zasu taba fitar da ku daga shiriya ba ba kuma zasu taba dawo da ku cikin bata ba� idan suka yi kasa ku yi kasa idan suka tashi ku tashi� kada ku riga su sai ku bata, kada ku yi jinkirin binsu sai ku halaka�[36].

7- Fadinsa (A.S): �� Shin ban yi aiki a cikinku da alkawari mafi girma ba, kuma na bar muku (na yi muku wasiyya da) alkawari mafi karanta�[37].

Alkawari mafi girma shi ne Kur�ani, alkawari mafi karanta su ne Ahlul Baiti (A.S) da su ne imam Ali (A.S) da Fadima (A.S) da imam Hasan (A.S) da imam Husain (A.S).

8- Fadinsa (S.A.W): �Mahadi daga cikinmu yake Ahlul Baiti, Allah zai tayar da shi a dare daya�, Ahmad da Suyudi sun rawaito shi daga Ali (A.S)[38].

�Mahadi daga garemu yake �ya�yan Fadima�, Suyudi ya karbo shi daga Ali (A.S)[39].

Haka nan wadannan mahadi suka zo da ga hadisai masu yawa da bayanai a fili da ishara da siffa da kuma bayanin tarihi tabbatacce.

A takaice muna iya cewa matakin imam Ali (A.S) da yakininsa na hakkinsa a game da halifanci ya kasance yakini ne wanda yake ya samu daga matsayinsa gun Annabi (S.A.W) da kuma rayuwarsa ta hidima ga musulunci, hakika ya kasance a rayuwar Manzo (S.A.W) yana cewa: Allah madaukakin sarki yana cewa; �Idan ya mutu ko aka kashe shi sai kuka juya akan duga-duganku[40] (kuka bar tafarkinsa)�, Imam Ali (A.S) yana cewa: �Wallahi ba zamu juya akan duga-duganmu ba, bayan Allah ya shiryar da mu, wallahi idan ya mutu ko aka kashe shi, sai na yi yaki akan abin da ya yi yaki akai har in mutu, wallahi ni ne dan�uwansa kuma waliyyinsa dan amminsa mai gadon iliminsa, wanene ya fi cancanta da shi fiye da ni�[41].

A wani wajen Ali (A.S) yana cewa: �yayin da ya rasu (S.A.W) sai musulmi suka yi jayayya akan mulkinsa bayansa, wallahi bai taba fado mini ba, ban kuma taba tunanin cewa larabawa zasu kawar wannan jagoranci a bayansa daga Ahlin gidansa! Ban taba tsammanin za a kawar da shi daga gareni ba bayansa! Sai ga mutane sun yi dafifi ga wane suna yi masa bai�a��[42]. Ashe kenan yana nufin hakkin da mutane suke nemansa, shi kuma ba ya rigonsu zuwa ga nemansa�[43].

Hafiz Muhammad Sa�id
[email protected]

[1] - Sharhin Nahajul Balaga Na Subhi Salihi: 12, 18, Da Na Abil Hadid: 10\128-129, Da Murujuz Zahab: 2\431.

[2] - Masnad: 1\84, 88, 181, Da Bidaya Da Nihaya Na Ibn Kasir: 5\229, Da 232, Da 7\383, 385.

[3] - Sunan Tirmizi: 5\3715, Da Sunan Kubra Na Nisa�i; 5\ H 8416.

[4] - Isti�ab: 3\35.

[5] - Kanzul Ummal: 5\724, H 14243.

[6] - Daga Zafir daga wani mutum daga�

[7] - Abdulwaris�

[8] - Kanzul Ummal: 5\726-727.

[9] - Sawa�ikul Muhrika: Babi 11, Aya 9, Da Manakib Na Khawarizimi: 213.

[10] - Sunan Nisa�i: 5\128, H 8461.

[11] - Nahajul Balaga: 97, Huduba 68.

[12] - Nahajul Balaga: 2-5, Hikam: 190.

[13] - Ibn Abil Hadid ya karbo daga Malminsa yana cewa da shi: Wallahi na samu wannan huduba a cikin wani littafi da an rubuta shi kafin a haifi Sharif Rida da shekara dari biyu.

Ya ce mun same ta a littafin Abil Kasim Albalkhi daga malaman Bagadad na daga mu�utazila da an haife shi a shekara 279, ya rasu a 317, Shi kuma Sharif Radi an haife shi ne a 360, An kuma rawaito ta a Tazkiratul Khawwas: 124, da Minhajul Bara�a: 1\131-132.

[14] - Kamar yadda akan sakaya labule domin shamaki daga abu, haka nan imam Ali ya kawar da kai ya rufe idonsa ya cije ya hakura.

[15] - Fadin Halifa Ku Karbi Bai�arku! Ku Karbi Bai�arku!

[16]- Kashe mu raba kan rike min kahonsa in tatsa in na gama sha in ba ka.

[17] - Nahajul Balaga: Huduba 3.

[18] - Nahajul Balaga: 102, Huduba 74.

[19] - Wajan yaki.

[20] - Mutumin da umar ya ba shi jagorancin mutane hamsin ranar shura domin su kashe wanda ya sabawa jama�ar da Abdurrahamani Dan Aufi yake cikinta.

[21] - Nahajul Balaga, Sharhin Ibn Abil Hadid: 6\167-168.

[22] - Nahajul Balaga: 246 Huduba 172.

[23] - Sharhin Ibn Abil Hadid: 9\305.

[24] - Nahajul Balaga: 246, Huduba 172.

[25] - Nahajul Balaga, Ibn Abil Hadid: 1\307.

[26] - Nahajul Balaga: 231, Huduba 162.

[27] - Nahajul Balaga: 497, Hikam 147.

[28] - Sharhin Nahajul Balaga: 18\351, Huduba 143.

[29] - Nahajul Balaga: 47, Huduba 2.

[30] - Nahajul Balaga: Huduba 88 Da 183.

[31] - Alhilafa Wa Nasha�atul Mazahibil Islamiyya Dr Muhammad Ammara: 33, 157-158.

[32] - Ma�alimut Tanzil, Albagawi, 4\278, Da Alkamil Fit Tarih, Ibn Asir: 2\64.

[33] -�Nahajul Balaga, Dr Subhi Salih: 201, Huduba 144.

[34] - Nahajul Balaga Dr Subhi Salih: 119, Huduba 87.

[35] - Tarihin Ya�akubi;� 2\211-212.

[36] - Nahajul Balaga 143, Huduba 97.

[37] - Nahajul Balaga 119, Huduba 87.

[38] - Masnad Ahmad: 1\84, Da Jami�ussagir: 2\672 H 9243.

[39] - Masnad Fatima, Suyudi: H 93\224.

[40] - Ali Imrana: 144.

[41] - Almustadrak: 3\126, Majma�azzawa�id: 9\134.

[42] - Nahajul Balaga: 451, Alkitab 62.

[43] - Fatima Wal Fadimiyyun,� Na Abbas Mahmud Akkad, M2, 326.